‘Yan sanda Sun Samu Nasarar Ceto Mutane 2 Da Aka Yi Garkuwa  Da Su A Zamfara

‘Yan sanda Sun Samu Nasarar Ceto Mutane 2 Da Aka Yi Garkuwa  Da Su A Zamfara
Gov. Zamfara

‘Yan sanda Sun Samu Nasarar Ceto Mutane 2 Da Aka Yi Garkuwa  Da Su A Zamfara

Daga Comr Zulq Bashir Gusau

‘Yan sandan jihar Zamfara sun samu nasarar ceto mutane 2, bayan makonni 2 da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ya bayyana,

A cewarsa rundunar ta samu nasarar ne bayan gudanar da bincike inda aka nemo su bayan sace su da a ka yi a Kaura Namoda an gano su a dajin Dumburun da Gidan Jaja da ke karamar hukumar Zurmi
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba N. Elkanah ya jajanta wa wadanda lamarin ya faru da su akan wahalhalu da azabar da su ka fuskanta a lokacin da su ke hannun ‘yan bindigan,

Sojojin sama sun gano mabuyar ‘Yan bindiga a kauyukan Kaduna, sun buda masu wuta

A wata takarda da Mohammed Shehu, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya gabatar wa Premium Times ya ce sun gudanar da bincike ne sannan su ka gano inda su ke.

Bisa ruwayar Premium Times, an sace su ne a Kaura Namoda sannan an ceto su a dajin Dumburun da Gidan Jaja da ke karamar hukumar Zurmi.

Kakakin ya bayyana yadda aka mika su asibiti don duba laifiyar su bayan nan su ka tattauna da ‘yan sanda.

Kamar yadda takardar ta zo Kwamishinan ‘yan sanda, Ayuba N. Elkanah ya jajanta wa wadanda aka ceto sakamakon wahalhalun da su ka sha lokacin su na hannun ‘yan bindigan.

Ya tabbatar wa jama’an jihar cewa da taimakon ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro za su tabbatar sun yi aiki tukuru don kawo garanbawul akan matsalar garkuwa da ke faruwa a jihar.

Kwamishinan ya yi kira ga jama’a akan su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai don ganin bayan duk wasu ‘yan ta’adda da ke jihar.

Duk da dokokin tsaro, ‘yan bindiga sun ci gaba da aika-aika
Jihohi kamar Zamfara, Katsina, Sokoto da Kebbi da ke yankin arewa maso yamma da jihar Neja ta arewa ta tsakiya, suna fama da rashin tsaro mai tsanani kusan shekaru 10 kenan.

Bayan dokokin tsaro da gwamnonin jihohi su ka dauka, har yanzu ‘yan bindiga su na ci gaba da kai wa mutane farmaki ta hanyar garkuwa da jama’a.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.