Wata 7: Masu Lalura ta Musamman Sun Yi Kira Ga Gwamnatin Sakkwato Ta Biya Su Bashin Alawus dinsu

Shugaban ya zayyano wasu matsaloli da suke fama da su musamman rashin zuwan 'ya'yansu makaranta da tsayawar cibiyar koyon sana'o'in yaransu da ta daina aiki, don haka suke son gwamnati ta kara duba yanayin da suke ciki. "Ko tallafin da gwamnatin tarayya take bayarwa har yanzu ba wani mambanmu da ya samu mun yi ta cika fom amma shiru ba wanda aka baiwa,"a cewarsa.

Wata 7: Masu Lalura ta Musamman Sun Yi Kira Ga Gwamnatin Sakkwato Ta Biya Su Bashin Alawus dinsu

 

Kungiyar masu lalura ta musamman da suka kunshi Makafi ta Guramu sun yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwato ta biya bashin alawus dinsu da suke biya tsawon wata bakwai.

Alawus din da gwamnati ke ba su a kowane wata 6500 yanzu an share watanni ba a biya ba, kan haka suke jan hankali da gwamnati ta waiwaye su domin wasu a cikinsu sun dogara da tallafin ne da yake hana masu yawon bara.

Shugaban kungiyar Haruna Muhammad Helele amadadin mambobinsa ya nemi gwmnati ta cigaba da ba su tallafin da aka tsayar, an daina ba su a wasu watanni da suka gabata.
Shugaban ya zayyano wasu matsaloli da suke fama da su musamman rashin zuwan 'ya'yansu makaranta da tsayawar cibiyar koyon sana'o'in yaransu da ta daina aiki, don haka suke son gwamnati ta kara duba yanayin da suke ciki.
"Ko tallafin da gwamnatin tarayya take bayarwa har yanzu ba wani mambanmu da ya samu mun yi ta cika fom amma shiru ba wanda aka baiwa,"a cewarsa.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha ta dube su a halin da suke ciki don a share masu hawaye.
Inno Asarakawa ta ce suna bukatar a kula da yaransu a harkar karatu kamar yadda aka yi alkawali, yanzu almajirai mata sun daina bara domin tsiratar da mutuncin yaransu mata.
Mai baiwa gwamna shawara kan lamurran masu lalura ta musamman Abdul'aziz Ibrahim ya ce mutanen su yi hakuri nan ba da jimawa za a biya su hakkinsu, ana kan kokarin ganin an biya su.