Tsarin Managarciya (Private Policy)

Managarciya mujalla ce dake bayar da labarun abubuwan da suke faruwa a Duniya gaba ɗaya musamman waɗanda suka shafi mata. Ba ta buga labarun ƙarya ko ƙazafi ko cin fuskar wani, ba a Samar da ita domin cin zarafin kowa ba, sai don kawo cigaba a cikin al’umma. Managarciya ba ta buga labarun batsa ko sanya hotunan tsiraici, duk labarun da suka saɓawa dokar aikin jarida na Nijeriya ba a buga su a Managarciya.

Ba wani ɓangare na rayuwa da mujallar ba ta buga labarinsa Wanda addini da al’ada suka aminta a yi bayani kansa. Managarciya a Online tana ƙoƙarin bin dokokin babbar manhajar Google a wurin hulda da jama’a domin gamsar da masu bibiyar shafin Managarciya.

Muhammad Muhammad Nasir Edita.