Tabbas Naji Kunya Kuma Nayi Takaici Akaro Na Biyu Kan Abunda Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Wa Al'ummarmu Ta Sokoto

Tabbas Naji Kunya Kuma Nayi Takaici Akaro Na Biyu Kan Abunda Shugaban Kasa Buhari Ya Yi Wa Al'ummarmu Ta Sokoto

 

Sokon majidadin Datti Assalafiy.

 

Dayawan mutane sukan dauka cewa bana damuwa da halinda kasar mu da Arewa ke ciki ne dan saboda nakasance  masoyin  shugaban kasa Muhammad Buhari  wanda kuma  ba haka ba ne.

 

Kowane  Dan Adam da yadda yake fahimtar rayuwa sanan ba yadda za ka dauki fahimtar wani ta yi daidai da taka hakan nada matukar wahala, amatsayina na Dan Adam mai hankali da kuma tunani daidai da yadda Allah Ya so nakasance nakan yi wani tunani kamar haka, duk wanda Allah Ya bashi shugabanci Allah Ya bashi wani yanki ne na kalifancin saboda haka Allah ne kadai zai yi dai dai da yadda mutane ke so ba dan Adam ba. Tunani na shi ne Buhari Masoyi ne nakasar mu ba makiyi ba, saboda haka ba zai iya nunawa kowa soyayya ba har kagane yana kaunar ka sai da mataimaki.

 

Buhari a maganar gaskiya baisamu mataimaka ba amma kuma shima yanada rauni amatsayinsa na shugaba amma mukan yi masa uzuri domin kowace rayuwa tana bukatan uziri sai dai wanan karo sai mun kausasa lamarin mu amatsayin mu na masoyansa.

 

Ace an kashe mutum 25  a sokoto baka je ba dan Allah ka kara kaimi ina rokon Allah Ya sa ka gane wanan kuskuren kuma ka gyara.

 

#sokotoenoughisenough