Ta Rasa Ranta Sakamakon Ƙonata Da Wuta Da Ɗan Cikinta Ya Yi

Bayan Steven ya tabbatar da aika-aikarsa, ya tsere. Ganin halin da ta shiga ta fito wajen tana kuwar neman taimako, kafin a kawo mata daukin dukkan ilahirin jikinta ya kone, ganin haka yasa aka garzaya da ita asibiti dan daukar matakin gaggawa. A ranar juma'ar nan, Madam Comfort ta rasa ranta sakamakon wannan aika-aikar da dan ta yai mata da misalin karfe uku na yamma. Bincike dai ya tabbatar cewar Steven Jiya ya sha yunkurin hallaka mahaifiyar ta sa amma bai cin ma nasarar hakan ba, sai a wannan lokacin.

Ta Rasa Ranta Sakamakon Ƙonata Da Wuta Da Ɗan Cikinta Ya Yi
Ta Rasa Ranta Sakamakon Ƙonata Da Wuta Da Ɗan Cikinta Ya Yi
Daga Babangida Bisallah, Minna
Mazauna unguwar Darussalam a yakin Kpakungu cikin karamar hukumar Chanchaga sun wayi gari cikin firgici da kaduwa sakamakon labarin yadda Steven Jiya ya bankawa mahaifiyarsa Madam Comfort Jiya wuta.
Binciken da wakilin Managarciya yayi, ya samu labarin cewar ranar littinin din da ya gabata ne Steven ya dawo daga Suleja ta jihar Neja, bayan dawowarsa ne lamarin ya faru inda ya kaiwa mahaifiyar ta sa da ke aiki a kicin farmaki.
Marigayiya Madam Comfort, tsohuwar malamar makaranta ce da ta taba shugabantar makarantar sakandare a jihar Neja da ta taba wata sakandaren gwamnàti a Sabon-Wuse da cikin garin Minna. Steven ya samu nasarar bankawa mahaifiyarsa wuta ne a lokacin da ke tsaka da yin girki, inda bayan ya zuba mata fetur ya cin na ma wuta a gidanta da ke Darussalam na yankin Kpakungu.
Bayan Steven ya tabbatar da aika-aikarsa, ya tsere. Ganin halin da ta shiga ta fito wajen tana kuwar neman taimako, kafin a kawo mata daukin dukkan ilahirin jikinta ya kone, ganin haka yasa aka garzaya da ita asibiti dan daukar matakin gaggawa.
A ranar juma'ar nan, Madam Comfort ta rasa ranta sakamakon wannan aika-aikar da dan ta yai mata da misalin karfe uku na yamma.
Bincike dai ya tabbatar cewar Steven Jiya ya sha yunkurin hallaka mahaifiyar ta sa amma bai cin ma nasarar hakan ba, sai a wannan lokacin.
Ofishin yan sanda na unguwar GRA sun yi nasarar cafke mai laifin inda bayan kai kotu, aka tura keyarsa gidan gyara hali da ke Minna.