Shirin Kwana 90: An Canja Salma Ne Don Ba Ta Da Ra'ayin Cigaba Da Shirin 

Shirin Kwana 90: An Canja Salma Ne Don Ba Ta Da Ra'ayin Cigaba Da Shirin 
Daraktan shirin shirin wasan kwaikwayo mai dogon zango, Kwana Casa’in, Salisu T. Balarabe, ya baiyana dalilinsa na sauya Maryuda Yusif, tauraruwar da ke haskawa a shirin, wacce ta fito da suna Salma, abin da bai yiwa makallatan shirin daɗi ba.
A wata hira da BBC Hausa, daraktan ya ce, tauraruwar ce da kanta ta baiyana cewa ba za ta ci gaba da fitowa a shirin ba saboda sirri da ya shafi gidansu.
"A tsarinmu na kwana 90, duk lokacin da za a gabatar da wani zango, akan tuntubi jarumai kafin lokaci, cewa an sa lokacin da za a ɗauki wannan zangon; waɗansu sukan faɗa cewa ba za su samu yi ba, saboda yanayi na karatu ko kuma wani dalili da su suka bar wa kansu sani, akan ba su wani lokaci in har suna son cigaba da fita a shirin", a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa, ”Lokacin da muka tuntuɓi Salma a kan cewa za mu ɗauki shirin Kwana Casa’in Zango na Shida ta fada mana cewa gaskiya ba za ta samu dama ba, mun so mu san dalili sai ta fada mana cewa ya na da nasaba da iyayen ta, wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa ba.” Inji Salisu T. Balarabe.
Rashin bayyanar Salma a shirin ya rage masa armashi sosai, wasu da yawa sun jingine kallon shirin don ya zama lami.
Wannan lamarin ya sha faruwa a duniyar wasan Hausa wurin sauya jarumai a cikin shirin da ya samu karɓuwa.