Sanata Wamakko Jagoran Jama’a Ne---Malamin Jami’a

Sanata Wamakko Jagoran Jama’a Ne---Malamin Jami’a
Sanata Wamakko

Malamin jami’ar Crownhill dake garin Ilorin jihar Kwara ya bayyana Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a matsayin jagoran jama’a.

Malamin jami’ar ya yi hakan ne a lokacin da yake karantar da dalibbansa a cikin aji,  ya ba da misali da tsohon Gwamnan Sakkwato  ne kan hidimarsa ga sha’anin ilmi domin Nijeriya na bukatar ire-irensa don ciyar da kasa gaba.

A wani faifan bodiyo da Managarciya ta yi kicibis da shi a kafofin sada zumunta malamin ya ce ‘na tabbatar da cewa yanda Sanata Wamakko ya yi hobbasa a wurin bunkasa ilmi, da jihohin kasar nan sun samu rabin abin da ya aiwatar da cigaban da ake da shi ya wuce haka, shi jagoran jama’a ne,’ a cewarsa.

Bidiyon mai dakika 55 ya nuna yanda Sanata Wamakko ya bar tarihi mai kyau a haujin ilmin jiharsa, da har ya yi naso a wasu jihohin Nijeriya ake yaba kokarinsa, da yi wa Sakkwatawa sam barka na samun jagora mai hangen nesa wanda burinsa ya tsaya kan cigaban al’ummarsa ne kawai.

Kalaman malamin wani kalubale ne ga masu rike da madafun iko a yanzu, su  sani kwatantawa da samar da cigaba irin na Wamakko ne yakamata su mayar da hankali kansa, don haka ne kawai zai sa ba za a taba mantawa da su ba, a kullum za a rika yi masu addu’ar samun gafara da yafiya ta ubangijinsu.