Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso  A APC?

Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar APC batare da tunanin da yawan al'umma ba. Sai dai wasu na danganta hakan da rikicin sa da Ganduje. Wasu kuma na ganin tsarin samar da Shugabanci a Jam'iyyance alokacin da kuma gaba, zai bashi matuƙar matsala da shi da Shekarau a jam'iyyar APC. Koma dai mene ne mu aje wannan batu a gefe. Kwankwaso yayi takarar cikin gida ta neman Shugabancin kasa a PDP, amma bai samu nasara ba, ba kuma zai haƙura ba. Amma tambayar anan shi ne, mece ce nasararsa bayan Atiku, Gwamna Tambuwal na Sokoto, da kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki da alamu suna gabansa a cikin jam'iyyar PDP, don haka dole ne Sanata Kwankwaso ya  buga sabon lissafi domin ganin mece ce makomar sa a zaɓen 2023, kuma wace jam'iyya ce yake da damar samun hakan?

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso  A APC?
Kwankwaso
Ko tantama bana yi Kwankwaso zai fi ƙaunar kasancewa a jam'iyya mai mulki, fiye da jam'iyyar da yake ciki ta PDP. 
A matakin da Kwankwaso yake yanzu, ya yi wa siyasar Jiha nisa, sai dai tunanin wane ne-da-wane ne suka dace ya dafa musu domin cimma burikan siyasar su. Matakin sa yakai a yi gogayya da shi wajen neman kujerar Shugaban ƙasa, ko Shugabancin Majalisar Dattijai. Wannan shi ne matakin mutumin da yayi ɗan Majalisa a jamhuriyar baya, ya Kuma mulki Jiha kamar Kano sau biyu, sannan kuma ya zama har Ministan tsaro, ɗaya daga cikin kujera mai daraja a Kasar nan.
Bisa ga dukkan alamu sai an yi sabon auren siyasa a Jihar Kano. Babu ko tantama hakan sai ya faru. Walau dai Kwankwaso ya Koma dinkewa da abokin siyasar sa Gwamna Ganduje, ko kuma ya dinke da abokin adawarsa Sanata Ibrahim Shekarau. Wannan alamu ne dake nuna za'ayi siyasa mai matuƙar mamaki da jan hankali wannan lokacin a zaɓen 2023.
A iya fahimtar da na yiwa shige-da-ficen Kwankwaso, da kuma tsarin siyasar sa. Ba burin gina mulki a Jihar Kano ne kaɗai ke gabansa ba, shi ma akwai burin ganin ya samu wata babbar kujera a sama, domin gudummawar da ya bayar a baya, ya ɗora a ci gaba. Don haka yana da buƙatar dama da za ta bashi wannan domin yaga ya cimma wannan burin.
Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar APC batare da tunanin da yawan al'umma ba. Sai dai wasu na danganta hakan da rikicin sa da Ganduje. Wasu kuma na ganin tsarin samar da Shugabanci a Jam'iyyance alokacin da kuma gaba, zai bashi matuƙar matsala da shi da Shekarau a jam'iyyar APC. Koma dai mene ne mu aje wannan batu a gefe. Kwankwaso yayi takarar cikin gida ta neman Shugabancin kasa a PDP, amma bai samu nasara ba, ba kuma zai haƙura ba. Amma tambayar anan shi ne, mece ce nasararsa bayan Atiku, Gwamna Tambuwal na Sokoto, da kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Bukola Saraki da alamu suna gabansa a cikin jam'iyyar PDP, don haka dole ne Sanata Kwankwaso ya  buga sabon lissafi domin ganin mece ce makomar sa a zaɓen 2023, kuma wace jam'iyya ce yake da damar samun hakan?
Rinjayen masu hasashe ya nuna PDP daga Arewa zata futar da dan takarar Shugaban ƙasa, akwai alamun tsakanin Atiku, Bukola da Tambuwal cikinsu ne za'a samu ɗan takara. Sa'annan akwai kishin-kishin din cewar tabbas APC zata cika alƙawarin ba da takarar Shugaban Kasa ga Kudancin ƙasar nan ne. Wanda ake tunanin akwai yiwuwar a marawa Osinbajo ko Amaechi baya, duk da cewar akwai masu ganin har yanzu takara ta Bola Tinubu(Jagaban) ita ce gaba, tau amma idan Jagaban yayi takara,  zai yi wuya a yi Muslim-Muslim ticket, wannan shi ne lissafin zaman Gwamnan Filato Lalong, Shugaban Gwamnonin Arewa, da kuma dawowar tsohon Kakakin Majalisa Yakubu Dogara jam'iyyar ta APC, saboda shi Tinubun ya samu Mataimaki daga Arewa. To amma zance mafi shahara ya tabbatar da cewa jigajigan jam'iyyar tuni sun fara shirin suntule Jagaban cikin wadanda ka iya zama yan takara a jam'iyyar.
Duk idan muka bibiyi wannan dogon sharhin, muna magana ce akan damar da Kwankwaso yake da ita wajen cimma ƙudurinsa na siyasa. Dawowarsa jam'iyyar ta APC, tamkar wata dama ce dake nuna zai iya ƙoƙarin ganin ya samu kujerar Mataimakin Shugaban ƙasa, sakamakon bataliyar masoya da yake da ita, da kuma kasantuwar yawan ƙuri'un da Kano take dashi, da kuma irin wanda dalilinsa za'a samu  Arewa.
To amma inda ƙalubalen yake, Gwamnonin dake ganin daga wannan shekarar sun sauka daga kan mulki, suma suna da wannan burin tuntuni na ganin cewar dole Mataimakin Shugaban ƙasa daga tsaginsu za'a ɗauka. Akwai Badaru na Jigawa, da Bagudo na Jihar Kebbi, sai Mai Mala da yake ganin karensa ya kai tsaiko tunda har ya iya riƙe Shugabancin jam'iyyar na riƙo, kuma a baya ya zama Sakataren Jam'iyyar na ƙasa. Akwai kuma tsagin Gwamna Elrufa'i na Kaduna, da kuma ɓangaren Minista Shari'a na ƙasa Abubakar Malami, duk da wasu na hangen shi kujerar Gwamnan Jihar sa ta Kebbi kawai ta isa rufe masa baki........ 
Wannan hasashen shi ne yake nuna cewar ba za su amince wani ya shigo jam'iyyar gabanin zaɓe, kuma ya amshe kujera mai daraja irin haka ba. Wannan su ne ƙalubalen da ka iya faruwa wajen cimma ƙudurin Shugaban Dariƙar Kwankwasiyya na Duniya.
 
Sunusi Mailafiya.