Sanata Barau Maliya Ya Rabawa 'Yan Wasan Hausa Motoci Da Babura A Kano

"Ina kira gareku da  ku dage wajen shirya finafinai masu inganci na addini da Al'adunmu domin tushe duk wata kafa ta koke-koke daga mutanen mu, babban burinmu a matsayinmu na iyayenku shi ne, wannan sana'a ta ku ta bunkasa ta hau matsayi babba a duniya", inji Farfesa Hafizu Abubakar. Da ya ke wakiltar dimbin Jaruman da suka halarta Jarumi Ali Nuhu ya ce da yawa daga cikin ƴan Kannywood dama ƴan jam'iyyar APC ne tun a 2015, don haka tafiyar Sanata Barau Maliya ba yanzu suka fara ba, kuma ƙuri'arsu ta zaben gwamna 2023 a Kano ta sa ce. Ali Nuhu ya godewa sanata da irin wanan kaɓakin alheri da ya baiwa ƴaƴan wannan masanarta ta Kannywood wanda zuwa ƴanzu babu wanda ya taɓa yi sai Maliya,

Sanata Barau Maliya Ya Rabawa 'Yan Wasan Hausa Motoci Da Babura A Kano

 

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

 

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya wato Sanata Barau I. Jibrin da aka fi sani da  Maliya, ya yi taron bayar da tallafi ga Ƙungiyoyin finafinan Hausa na Kannywood.

 
Taron wanda ya gudana a ranar Lahadin makon jiya  a dakin taro na Mina Event Center da ke cikin birnin Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamared Isayaku Abubakar Balan da kuma Jami'in shirye-shirye Honarabul Basiru Yusuf Shuwaki wanda shi ne shugaban Kano Progressive Media Network (Kapmen)
 
Tun da farko a jawabinsa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, wanda ya wakilci Sanata Barau Farfesa Hafizu Abubakar ya ce wannan tsari na mai girma Sanata kan tallafawa ɓangarorin Al'umma a rayuwarsu ba ƙaramin abu ba ne a jihar Kano kuma shi ake  buƙata. 
Ya kara da cewa, "Na zo wajen taron nan ne saboda na gamsu cewa anan gaskiya take, kuma Sanata Barau al'umma ne a zuciyarsa.
 
"Ina kira gareku da  ku dage wajen shirya finafinai masu inganci na addini da Al'adunmu domin tushe duk wata kafa ta koke-koke daga mutanen mu, babban burinmu a matsayinmu na iyayenku shi ne, wannan sana'a ta ku ta bunkasa ta hau matsayi babba a duniya", inji Farfesa Hafizu Abubakar.
 
Da ya ke wakiltar dimbin Jaruman da suka halarta Jarumi Ali Nuhu ya ce da yawa daga cikin ƴan Kannywood dama ƴan jam'iyyar APC ne tun a 2015, don haka tafiyar Sanata Barau Maliya ba yanzu suka fara ba, kuma ƙuri'arsu ta zaben gwamna 2023 a Kano ta sa ce.
 
Ali Nuhu ya godewa sanata da irin wanan kaɓakin alheri da ya baiwa ƴaƴan wannan masanarta ta Kannywood wanda zuwa ƴanzu babu wanda ya taɓa yi sai Maliya,
 
An dai rabawa jaruman Kannywood da mawaƙa Motoci guda 17, da  Babura guda 100, sai Na'urar Kwamfuta (laptop) guda 80.
 
Daga cikin wadanda suka rabauta da Motoci sun hada da:
Ali Nuhu, Adam A. Zango,Hajara Usman,Yakubu Muhammad,Fati Muhammad, Dan ƙuda, Baba Ari, Ado Gwanja, Falalu Dorayi da sauransu.
 
Taron dai ya samu halartar shugaban Jam'iyyar APC tsagin Sanata Mal. Ibrahim Shekarau, Hon. Amadu Haruna Zago, Hon. Murtala Alasan Zainawa da Hon. Shitu Madaki Kunchi da Hon. Yusuf Tumfafi, da Hon. Abdullahi Magaji Lamba Bichi, da Hon. Dan Sharu Bebeji, da Hon. Isyaku Abubakar 
 
Daga karshe dai masu  Barkwancin nan (Baba Ari) da su Daushe sun gabatar da takaitaccen wasan kwaikwayo a wurin, taron dai ya samu halartar jarumai maza da Mata da ke masana'antar shirya Finafinai ta  Kannywood.