Sakkwato Ta Kara Samun Cigaba:Haruna Dasuki Ya Samu Karin Girma Zuwa Birgediya- Janar 

Sakkwato Ta Kara Samun Cigaba:Haruna Dasuki Ya Samu Karin Girma Zuwa Birgediya- Janar 

 

Kanal Haruna Ibrahim Dasuki yana cikin manyan jami'an soji da suka samu karin girma daga mukamin Kanal zuwa Birgediya- Janar. 

 

Likkafan sojan wanda ke da kwarewa da gogewa a tsawon shekaru ta kara samun daukaka ne a yayin da Rundunar Soji ta aminta da karin matsayinsa daga Kanal zuwa Birgediya-Janar bayan cike dukkanin matakai da ake bukata.

 
A Rundunar Soji Kanal 76 ne suka samu karin girma zuwa Birgediya-Janar kamar yadda Majalisar Koli ta Soji ta aminta a zamanta na ranar 21 ga Disamba.
 
Mukaddashin Daraktan Yada Labarai na Rundunar Soji, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a ranar Laraba yana cewar karin girman ya biyo bayan amincewar Majalisar Soji a jiya 21 ga Disamba. 
 
Birgediya- Janar H.I Dasuki, da ne ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi na 18, Dakta Ibrahim Dasuki dan Halliru dan Bara'u dan Mujaddadi Shehu Dan-Fodiyo.
 
A rana irinta jiya ce a shekarar 2016 lokacin da Haruna Dasuki ya samu karin matsayi, Hon. Abdussamad Dasuki wanda a wancan lokacin shi ne Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa a Majalisar Wakilai kana wakilin Kebbe/Tambuwal ya daura masa karin girma zuwa Kanal.
 
 
 
Muryar Mazabar Kebbe/Tambuwal-8th Assembly