Rundunar 'Yan Sanda A Zamfara Ta Ceto Mutane 97 Hannun  'Yan Bindiga

Rundunar 'Yan Sanda A Zamfara Ta Ceto Mutane 97 Hannun  'Yan Bindiga

Daga Hussaini Ibrahim,Kauran Wali

 Rundunar 'Yan sandan Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Kwamishina CP Ayuba Elkana ta ceto mutane 97 a cikin ƙananan hukumomin Tsafe, Shinkafi, da Karamar Hukumar Sabon birni cikin Jihar Sokoto.

Kwamishina 'Yan sanda na Jihar Zamfara,Ayuba N.Elkanah ne ya tabbatar haka alokacin da ya ke amsar 'yan tatun a Gusau.

 Kuma ya bayyana cewa,mutane sitin da takwas, suna daga cikin wadanda gawurtacen dan ta'adda da ya addabi yankin Shinkafi watau Bello Turji.yayi garkuwa da su,a cikin su akwai Maza talatin da uku,Sai yara mata bakwai da "Yan mata ashirin.kuma wadanan sun fito ne daga Kananan hukumomin Shinkafi,Maradun Zurmi,Birnin Magaji Da Sabon birni cikin Jihar Sokoto.Inji Kwamishina CP Ayuba Elkana.

A cikin Karamar hukumar Tsafe,kuwa sun ceto Daliban Makarantar Islamiya ashirin da tara, daga hannun masu garkuwa da mutanan .a Kuma qaramar hukumar Gusau kuwa cikin garuruwan ,Adarawa,Gana,Bayawuri,yankin Rijiya sun ceto mutane 25 daga hannun'Yan Bindiga ayanzu Haka.

Kwamishina CP Ayuba ya bayyana nasarorin da Rundunar ke samu ne akan qarfafawar gyuwa da Sugeto Janar na"Yan Sanda ke basu da kuma tallafin gwamna Matawalle Maradun na ganin sun gama da 'Yan Bindiga da suka addabi jihar ta Zamfara.