Rashin Bashir Tofa Babban Rashi Ne Ga Ƙasar Nan------Shugaban Majalisar Dattijai

Rashin Bashir Tofa Babban Rashi Ne Ga Ƙasar Nan------Shugaban Majalisar Dattijai
 
Daga Babangida Bisallah, Abuja.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya aike da sakon ta'aziyar sa ga iyalan Alhaji Bashir Othman Tofa wanda ya rasu a ranar Litinin din makon nan.
Haka nan Lawan ya jajanta ma gwamnati da jama'ar jihar Kano a bisa rasuwar marigayin. Har ila yau ya mika ta'aziyar sa ga abokan hulda da na yan siyasa na marigayi Tofa. 
Shugaban majalisar dattawan yace rasuwar Bashir Tofa, wanda ya bayyana da kwararren dan siyasa, babbar asara ce ga kasar nan. 
Yace, "ina mai mika ta'aziya ga iyalan Alhaji Bashir Tofa da kuma gwamnati da jama'ar jihar Kano. 
"Alhaji Tofa ya bada gaggarumar gudummuwa a matsayin sa na shahararren dan siyasa kuma dan kasuwa. 
"Mutuwar sa babbar asara ce ba ga mutanen jihar Kano kawai ba har da kasa baki daya." 
Mista Ola Awoniyi
Mai ba shugaban majalisar dattawa shawara akan aikin jarida ya fitar da sanarwar talatar makon nan. Inda ya cigaba da cewar shugaban majalisar dattawan yayi addu'ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya sada shi da gidan Aljannah firdausi, ya kuma ba wadanda ya bari hakurin jure wannan rashi.