PDP Ta Sanya Ranar Zaben Arewa Maso Yamma Da Rikicikin Kwankwaso Da Tambuwal Ya hana Aiwatar Da Shi

PDP Ta Sanya Ranar Zaben Arewa Maso Yamma Da Rikicikin Kwankwaso Da Tambuwal Ya hana Aiwatar Da Shi

Jam'iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta sanya 12 ga watan Fabarairu ta zama ranar da za a yi zaben shugabanni a yankin arewa maso yamma wanda aka kasa gudanarwa kan rikicin shugabanci da ke tsakanin Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kan wanda zai zama mataimakin shugaban jam'iya a yankin. 

PDP ta sanya ranar zaben shugabannin yankin  da ba a yi ba domin cike wannan gibin na shugabanni. 

Wannan saka ranar ta zo bayan da shugabannin jam'iya suka zauna a ranar Laraba data gabata aka saka ranar kamar yadda sakataren tsare-tsaren jam'iyar Honarabul Umar Muhammad Bature ya sanar.
An aminta da gudanar da zaben a jihar Kaduna kuma duk wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyar za a sanar da su da ka'idojin zaben kamar yadda yakamata.

Wannan kusan shi ne karo na uku ana saka ranar zaben ana dagawa kan kasa sasanta rikicin dake tsakanin jagororin da alama tun aka saka wannan ranar an kai matsayar daidaito da ba a sake abin da ya faru a farko ba da taron ya watse ba cikin shiri ba.