Mun Fara Shirin Lashe Zaben Gwamnan Sakkwato A 2023----Ibrahim Mai Kassu Goronyo

Mun Fara Shirin Lashe Zaben Gwamnan Sakkwato A 2023----Ibrahim Mai Kassu Goronyo

 

Shugaban jam'iyar Boot Party  reshen jihar Sakkwato Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo a zantawarsa da Managarciya kan halin da jam'iyarsu take ciki a jiha ya bayyana cewa sun fara shirin yanda jam'iyarsu za ta karbi ragamar mulkin gidan gwamnatin jihar Sakkwato duba da yanda tafiyarsu ke samun karbuwa da kuma yanda mutane ke son sabbin jini dake da kwarewar a fannin mulki da siyasa.

 

"Bayan kammala karbar ayarin hukumar zabe da suka ziyarci ofishinmu dake kan hanyar gidaje 500 na Bafarawa, nuna gamsuwarsu da yanda tsarin jam'iya ke tfiya ya kara mana kwarin guiwa a wurin wayar da kan jama'ar jihar Sakkwato na su karbi wannan jam'iyya don ciyar da jihar Sakkwato gaba," a cewar Mai Kassu.

 
Shugaban ya jinjinawa jagororin jam'iyya da magoya bayansu a jiha tare da ba su tabbacin samun nasara a babban zabe na 2023 da ke tafe.
 
Mai Kassu ya ce a yanzu jam'iyarsu ta dukufa ga shiga lungu da sakon jiha domin wayarda kan jama'a kudurori da manufar tafiyar don mutane su zo a hada kai don kai jihar Sakkwato a tudun mun tsira.
 
Goronyo ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara matsa kaimi a yakin da take yi na kawar da 'yan bindiga a yankin Sakkwato ta gabas, domin har yanzu mutanen yankin na fuskantar matsalolin tsaro sosai.