MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Takwas

Mee'ad da Majeed sun shaku sosai kuma suna kaunar juna kamar su sace juna dan kuma ba wanda yake yin wani abu ba tare da dan uwansa yasan dame yake yiba shakuwa takai shakuwa harya zamana kullum Mee'ad batada 'abin kallo sai pictures din Yaya Majeed wanda ta tura ' a wayar Mommynta, ya kasance tin lokacin data tura pics din ta goge a wayar Mommyn kuma tace masa bata yadda ya kara tura pics dinsa ma kowa ba, ba tareda tsori ko fargaban komai ba ya 'amsa da to sbd zuciyarsa tana matukar kaunar Kanwartasa.  "Ta bangaren Majeed shima haka abin yake akwai hoton da suka dauka tare da Amal da kuma Mee'ad sun sanyashi a tsakiya suna dariya hoton yayi kyau sosai, wannan hoton shine ya zama abin kallon Majeed ba dare ba rana, kullum idonsa nakan hoton fuskarsa dauke da kayataccen murmushin jin dadin kuma ga dukkan alamu hoton na dauke masa kewan gida sosai.

MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Takwas
          _*MEE'AD*_
 
*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
 
 
  
        JINJINA & SADAUKARWA
 
Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
                        
                  
                           
                          
 
                    
 
                    
   
 
                      17 ~ 18
 
 
 
Karan shigowan text dinne yaja hankalin Mee'ad zuwa kan system din cikin zumudi ta dauki system din ta bude sako a rubuce kamar haka....
 
""" Ina cikin koshin lpy kanwata dftn kema haka ? Yau bakiga sakona ba karatune yashamin kai sosai, yaci gaba da cewa Kanwata wacce maganace a cikin ranki da har zaki iya boyema Yayanki farin cikin ki ita ? Ki fadamin ina saurarenki kinji kanwata,"
 
"Tana gama karanta text din lallausan murmushi tayi kafin kafin ta fara masa reply tana fadin " Yayana dama inaso kayi min alkawarin bazaka taba yadda ko soyayya da wata ya mace a fadin duniyar nan ba bayan wacce zuciyarka take muradi  kuma inaso kayi min alkawarin bazaka taba kallon pictures din muba har ranar da zaka gama makaranta ka dawo kasarmu. Tana gama rubutawa ta tura masa zuciyarta cike sa fargaban mi Yayan nasu zaice.
 
" Text din bai jimaba yayi mata reply da cewa yayi mata alkawarin hakan ba tare da wani fargaba ko nadaman yin wannan alkawarin ba.
 
Mee'ad da Majeed sun shaku sosai kuma suna kaunar juna kamar su sace juna dan kuma ba wanda yake yin wani abu ba tare da dan uwansa yasan dame yake yiba shakuwa takai shakuwa harya zamana kullum Mee'ad batada 'abin kallo sai pictures din Yaya Majeed wanda ta tura ' a wayar Mommynta, ya kasance tin lokacin data tura pics din ta goge a wayar Mommyn kuma tace masa bata yadda ya kara tura pics dinsa ma kowa ba, ba tareda tsori ko fargaban komai ba ya 'amsa da to sbd zuciyarsa tana matukar kaunar Kanwartasa. 
 
"Ta bangaren Majeed shima haka abin yake akwai hoton da suka dauka tare da Amal da kuma Mee'ad sun sanyashi a tsakiya suna dariya hoton yayi kyau sosai, wannan hoton shine ya zama abin kallon Majeed ba dare ba rana, kullum idonsa nakan hoton fuskarsa dauke da kayataccen murmushin jin dadin kuma ga dukkan alamu hoton na dauke masa kewan gida sosai.
 
                   
 
 
                  %%%%%%%%%
 
 
 
 
Amal ce zaune bisa kan kujera tana rera waka kamar wata shahararriyar mawakiya sai makalkale murya take da 'alama tanajin dadin wakar da takeyi sosai,"
 
Mommy ce ta sauko daga sama fiskarta dauke da murmushi tana cewa Amal sai wani makalkale murya kk kamar wata Fati Niger a Studio 
 
"Murmushi Amal tayi kafin tace Mommy yau inajin dadine sosai,  Mommy ta zauna a kujerar dake gefenta ta dafa kafadar Amal kafin tace Ya'ta miya sanyaki farin cikine haka ?" 
 
"Daria Amal tayi kafin tace Mom haka kawai na tsinci kaina cikin farin ciki Momy ta ce naji dadin hakan sosai ina Yar uwan taki ta shiga ne ?"
 
Amal tace tana bed karatu takeyi dan naga ta aika an sai mata wadansu novels,  murmushi Mom tayi kafin tace Allah shi kyauta bari naje kitchen ko ? To Amal tace kafin taci gaba da wakakokinta kamar wata zabiya.
 
Mee'ad! Mee'ad!! Mee'ad!!! Amal ce take kwala mata kira cikin zumudi take fadin to wai ina ta shigane kam ? Dakin Umma ta nufa da sauri tana kara kwalama Mee'ad kira, harta shiga cikin room din bara daina kwala mata kiran ba, da shigarta ta tarar da Umma zaune bisa gado tana waya,  a hanzarce ta juyo tana kara kwalama Mee'ad din kira,"
 
A kitchen ta tarar da Mee'ad tana taya mai girkinsu wanke2, taje da sauri ta rungume Mee'ad tana fadin albishirin ki" cikin zumudi Mee"ad tace goro fari tass ma daria Amal tayi kafin tace wannan term dinma ke kikazo first position,"
 
"Alhamdulillah Mee'ad tace kafin ta daka tsalle tare da rungume Amal dake gefenta, sai da sukayi murna mai isarsu kafin Amal tace kinga yanzu bamu da matsalar Waec da Neco ko ? Mee'ad tace kwaraima kuwa ni inaji a jikina mune zamu dauke gasar baki daya, daria Amal tayi kafin tace kinga kuma idan kika gama da wannan point din zaki samu duk irin course din da kk so a university," 
 
Alhamdulillah Mee'ad ta kara fadi kafin tace Allah mun gode maka kuma  bazamu taba gajiya da rokonka 'akan dukkanin al'amura muba har sai ranar da rai yayi halinsa  Allah ka dauki rammu muna masu imani kuma ka jikan dukkan masu imanin da suka rikamu amsa kira, mu kuma da muke a raye Allah ka dauki rammu muna masu imani dukansu suka amsa da Ameen, kafin Amal taja hannun Mee'ad zuwa falo.
 
Suka sami wajen zama a falo suna zama kuma suka fara tattauna batun fitarsu a secondary skull domin kuma Amal ta samu repeat ne ta koma ajinsu Mee'ad sukaci gaba da tafiya tare, wannan dalilin yasa suke dan zama su tattauna wadansu maganganun da suka shafi class dinsu tare,  duk dama Amal bata fiye sauraran Mee'ad a cikin skull ba sbd tana ganin kanta a matsayin babar yarinya wacce ta girme ma Mee'ad din, duk dama kusan kansu 1 sai tsayin da Amal ta fi Mee'ad kadan, amma girman jikinsu kam kamar tare suke girma, sun dan dade suna tattauna wan, bayan sun gama kuma kowacce ta nufi dakinta danyin sallan la'asar.
 
"Tin suna ss 1 Amal tasa aka raba musu room da Mee'ad sbd wai bata son takura.
 
"Hmm! Amal kenan yarinya kyakkyawa wankan tarwada bi ma'ana chocolate color tanada tsayi sosai kuma ta girma sosai dan kuma shekarunta zasu iya kaiwa irin 18 din nan, Amal yarinya sabon jini mai ji dakai yar gidan manyan mutane, gata da rawar kai da surutun tsiya,  zan iya  cema mai karatu ba wanda baisan rigimar Amal da group dinsu ba har suka kai ga  kammal secondary skull,  domin a group din manyan yara take kuma marasa ji' irinsu kawarta Amrah.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Pls fans don't forget to read, vote & share to other groups 
 
 
 
 
Love u much my fans
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Pls 
 
Fans
 
Ku
 
Nemeni 
 
Akan
 
Wannan 
 
No din
 
Dan bada shawara ko makamancin haka haka zalika idan kina/kana son shiga MEE'AD FANS GROUP.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Taku har kullum Hauwancyy Misau.