MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Goma

MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Goma
                        
                  
                           
                          
 
                    
 
                    
   
 
                           21 ~ 22
 
, , , , , , CIGABAN LABARI, , , , , , , , , , ,
 
 
          Karfe 4 dai2 agogon dake daure bisa hannun Mee'ad ya nuna dago kai tayi ta kalli Amal dake driving kafin tace Bloody 4 faah ta cika! 
 
"Ta juyo ta kalleta kafin tace aike kika jaa har wannan lokacin tayi, sunkuyar dakai Mee'ad tayi kafin tace toya muka iya kawai sauri zakiyi mu karasa mubama Umman Amrah sakon kinga saimu juyo da wuri ko ? 
 
Harararta tayi kafin tace ke kin gama naki uzurin na kuma jiraki shine kike son ki hanani aiwatar da nawa uzurin to hakan bazai yiyu ba gaskiya.  
 
"Murmushi Mee'ad tayi kafin tace nasan uzurin naki bashi da wani karfi ne shiyasa nace hakan, yatsina fuska Amal tayi kafin tace wannan kuma keya dama nima saina gama nawa uzurin kinji zancen gaskiya ko ? Shiru Mee'ad tayi bata kara cewa komai ba sbd tasan halin Bloody nata.
 
Suka danyi shiru na yan mintuna kafin Amal ta juyo tace waike agogon da kika sa muka bata lokaci wajen sayansa mawa kika sayawa ? Naga kamar na mazane ko ? Murmushi tayi kafin tace na sayama Mu'az na course din mune inaso nayi masa bazata ne,"
 
"Mtswww! Shirmen banza dai kawai zakiyi inji Amal."
 
"Sunkuyar dakai Mee'ad tayi bata kara cewa komai ba".
 
30minute after 4 dai2 suka isa gidansu Amrah,  horn Amal tayi mai gadi yazo da sauri ya bude get din, ta shiga tayi parking, cikin zumudi suka fita daga moton baki dayansu", 
 
Amal tana sauri dan taje su zanta da kawarta Amrah, yayinda Mee'ad take zumudin haduwa da Umman Amrah sbd tana koyon abu da yawa tare da Umman musamman girke2 da kuma dressing da sauransu,"
 
Da sallama suka shiga cikin falon gidan ai kuwa sunzo a sa'a dan kuma Umma na zaune da 'alamar kallo takeyi da gudu Mee'ad taje ta fada jikin Umma tana daria,"
 
"Fuskar Umma cike da farin ciki ta dago kai tana cewa yau mutuniya tace a gidan namu ai Hajiya ta kirani take tambayata kokun iso! Ashe kuna kan hanyane abinku daria sukayi baki dayansu kafin su gaishe da Umman cike da girmamawa, Umma ta 'amsa tana daria Amal ta mika mata sakon da Hajiyarta ta basu su kawoma Umman,  kafin tace Umma ina Amrah ?" 
 
Murmushi tayi kafin tace Amrah tana bed din...bata karasa maganar da take ba Amal ta tari numfashinta da cewa bari naje na sameta, bata jira jin amsar Umman ba ta shige ciki bata zame ko ina ba sai dakin Amran.
 
           %%%‰%%%%%‰%%%
 
Kwance ta tarar da Amrah bisa gado sai sharan bacci take ba 'abinda ke daminta," 
 
"Daka mata duka Amal tayi tana fadi ke yar iska tashi kiga na cika 'alkawarin gani a gidanku,  cikin magagin bacci Amrah ta bude ido ai kuma sai tayi arba da Amal cike da zumudi ta tashi ta zauna ta danyi ihu! Tana fadin shegiyar kawa sai yau kikaga daman zuwa ko ? Daria tayi kafin tace hmm kawata bari kawai Daddy ya hanamu sakat 2days din nan dan yaga muna hutun skull, Daria Amrah ma tayi kafin tace kawai sai naga kawata dodar a online sai naji wani hello!
 
" Amal tace ke in baki labari dakyar Daddy ya sai mana waya wai bayason shashanci kuma waya tana hana karatu bai san nikam na jima da yar " itel" dina a hand ba, shewa sukayi gamida tafawa  kafin Amrah tace Allah ya shiyaminke kawata Amal ta 'amsa da Ameen! Kafin tace yauwa musamman na hada wannan tafiyar yau dannazo mu gana dake sbd maganar bazata yiyu a waya ba, Amrah ta gyara zama tana fadin inajinki, taci gaba da cewa bana baki lbrn next week Yaya Majeed zai dawo kasar nan ba ?, 
 
"Amrah ta daka tsalle kafin tace wai da gaske kike ?, 
 
"Amal tace kwaraima kuwa! Amrah tace Alhmdllh kice burina zai cika, Amal tace idan kinsa himma ba,"
 
" Amrah tadan zare ido tana fadin ban gabe idan nasa himma ba ?, 
 
"Amal ta gyara zama kafin taci gaba da cewa jiya Abba da kansa ya kiramu nida Mee'ad yake shaida mana zuwan Majeed kuma yayi mana fada sosai gaskiya", 
 
" Amrah tadan ya tsine fiska kafin tace yanxu Abban da kansa ya shaida muku dawowar nasa ? Amal tace yanzufa na gama shaida miki hakan, Amrah tabe baki tayi kafin tace kawata nifaa ina tinanin wannan kiran da akayi mukun akwai manufar hakan gwalo ido Amal tayi kafin tace kamar yaya kenan ?, 
 
" Amrah tace bazaki ganeba sai gaba zan ganar dake kawallita  daria sukayi baki daya kafin Amrah taci gaba da fadin yauwa kawata inaso ki bani number Majeed pls yatsine fiska Amal tayi kafin tace kash!, 
 
"Ni kinga banada no dinshi ma gaskiya 'amma ina tinanin waccar shashashan tana da ita,  murmushi Amrah tayi kafin tace toki karba ki turamin kinji kawallina?, toh kawai Amal tace amma a zuciyarta take fadin haba ni zaki tambaya no dinsa kije ki nema da kanki dai danni nafi karfin nasa no dinshi a wayata!, 
 
" Amrah tace yaya bayanin waccan guy dinne ?, 
 
"Murmushi Amal tayi kafin suci gabada firarsu irin na kawaye.
 
A can cikin gida kuma Ummace zaune bisa kujera suna fira da diyarta Mee'ad ba abinda suke sai daria, Mee'ad ta nemo paper da biro Umma tanayi mata bayani akan yadda ake ;
 
, , , Lemon tsamiya da cucumber, , , 
 
Ingredients:
 
{1⃣} Tsamiya
{2⃣} Sugar 
{3⃣} Citta & Kanumfari
{4⃣} Kankara & Cucumber
{5⃣} Tiara & Flavour
 
Prapration:
 
     Da farko ki wanke tsamiyarki saiki zuba 'a tukunya kisa kayan kamshinki ki dafashi idan ya dahu saiki wanke cucumberki ki yanka kiyi blading dinta ki hada da tsamiya ki tace kisa flavour da sugar kisa tiara dinki sannan ki kawo kankara ki zuba a ciki idan babu kanakara kuma zaki iya sakawa a firiji yayi sanyi, yanada dadin sha sosai yar uwa ki gwada yima oga kisha santi.
 
"Bata dade da gama kwatanta mata yadda 'ake lemon ba su Amrah suka fito daria sukeyi suna fira, harara Umma ta doka musu kafin tace harkun gama gulman kenan ? Shiru sukayi basuce komai ba harta kara cewa to Amal kizo ku tafi yanzu sbd naga five ta wuce, Amal tadan bata fiska kafin tace haba Umma korarmu kikeyi ne ? Umma tace na koreku din maza ku wuce ku tafi tin kafin Daddy ya dawo ga sakon nan kikaima Hajiyar taki kinji ko ? Karban sakon tayi kafin tace to uwarsu saiki tashi mu tafiko ?"
 
"Batace komai ba ta mike ta nufi hanyar fita har tayi kusan fita ta juyo hade da cewa na gode sosai umma zan tambayi Mom ta bani time nazo mu yini  Umma tace ba komai ya'ta Allah ya kawoki lfy, Ameen tace kafin ta fita".
 
Har bakin moto Amrah ta rako Amal sunata zuba surutun banza da gulme2  samarinsu Mee'ad dai tanajinsu amma bata tanka musu ba hasalima wayarta ta dauko ta fara text chat da Yaya Majeed tana murmushi.
 
Amrah ta sako kai cikin moton ta zubama Mee'ad ido tana fadin bari naga dawa kike chat naga sai wani murmusawa kike fizge wayar dake hannun Mee'ad din tayi tana fadin sai naga da uban wa kike chat now, tana karbe wayar ta dora ido bisa kan screen din wayar ? Dago kai tayi cikin fushi take fadin kan uban can mi nake kallo haka ?.........
 
 
 
Pls fans don't forget to read, vote & share to other groups 
 
 
 
 
Love u much my fans
 
 
 
Taku har kullum Hauwancyy Misau.