MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Biyu

MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Biyu


          _*MEE'AD*_
                   
*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN

P.W.A

*THE BOOK IS WRITTEN*

*BY*

*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
  
Wattpad __@Hauwancyy44              

      

      JINJINA & SADAUKARWA


Gareki babbar Aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara basira da daukaka ya kuma kareki daga sharrin mai sharri.

                    *- Page -* 5 & 6

Haka lokaci yayita tafiya cikin ikon Allah Aliyu da Hisham suka kammala degree dinsu ko wanne a cikin su ya kama aiki Aliyu yafi karfi ta wajen kasuwanci yayinda hisham kuma ya kama office da kuma kasuwan baki daya," ita kuma karamar kanwarsu Ameena tana 1level a jami'ar bayaro dake nan kano.

Zaune suke baki dayansu a falo suna fira kasan cewar ranar week end ne,  Hajiya hindu sai murmushi take domin tafi kowa jin dadin yadda kan ya'yan nata yake a hade, Hisham ya kalli Hajiyar tasa kafin yace Hajiya waya kara baki kyautar kujerar makka 'a karo na 5 naga sai wani murmusawa kike  Hajiya hindu tace inaga kaina mai shirin bani wannan kujerar makkan tinda kafi kowa sakamin ido  dariya hisham yayi kafin yace haba hajiyata yaudin kuma ni nake sa miki ido.... Aliyu ya tari numfashin Hisham da cewa to idan ba sa idoba mi kk mata haka ? 

Amina dake gefe can hannunta rike da handout sai a lokacin tayi magana da cikin zolaya take cewa kaga yaya Aliyu karka takura ma yayana fakafin Aliyu yayi magana Amina tace yauwa ni yaya ya lbrn Aunty suby ne kaga ya kamata a hada bikin da nawa dan aji dadi sosai ko ? Aliyu yace kagamin yarinya ko kunya bakiji ko to sai anyi bikinki da 2 or 3 years da nayi aure kinga kafin na suby ta kara girma ta kuma gama skull ko ? Amina tace ai kuma da naji dadin hakan sosai duk dama halin subyn sai a silo harararta Aliyu yayi kafin yace to rufamin baki bance ki tabamin yar lelena ba, Hisham yace kai yaya banda rashin ta ido faa Hajiya tace barshi yayi abinshi muma munyi namu xamanin ai  Amina tace kunga barina baku guri sbd na farajin abinda yafi karfin jina tana gama maganar ta mike ta nufi dakinta Hisham yace kinga nima jirani ya rufa mata baya Aliyu yace kwayi tayi ai ya gyara xama sukaci gaba da hiransu da Hajiya.

Haka rayuwa ya kasance cikin jin dadi xumunci da bama juna kulawa har lokacin auren Aliyu yayi kasan cewan ya girme musu," Aliyu ya auri yar Abokin kasuwancin Abbansa mai suna Suwaiba suna kiranta da suby,  suby ya' 1 tilo wajen Alhaji kassim shima dan kasuwane kamar yanda Abban Aliyu ya kasance sai dai kusan xan iya cewa Alhaji kassim yafi Alhaji sa'ad tarin dukiya ta alfarma," 

Suby ta taso a sangarce batasan bari ba kuma batasan babu ba har ranar da mahaifinta ya aurar da ita ma dan Amininsa Alhaji sa'ad."Alhamdulillah ansha hidima an gama lfy yayinda Amarya ta tare a gidan mijinta dake unguwar gaida sai dai muyi musu fatan Allah ya basu zaman lpy.

Bayan bikin Aliyu da yan watanni aka aurar da Ameena kanwarsu, An aurar da Ameena ma wani Dr jamal dan kasan unguwarsu wanda tin tana yarinya yake dawainiya da soyayyar ta ba laifi ansha hidima mai tarin yawa kuma ankai amarya gidanta lpy.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin jin dadi hade da kwanciyar hankali, yayinda Hisham yake tare da Hajiyarsa a gida kullum yana kan shan gori.  

Shekarar Ameena 1 da Aure ta haifi santalelen yaronta kyakkyawa hak! fulani yaro mai kama da mamanshi da babanshi ya gado kyauwun fulanin asali ta ko wani gefe, murna a wajen family babu kama kafar yaro kasancewar Matar yaya Aliyu har wannan lokacin bata samu haifuwa ba." Wannan dalilin yasa bebyn da aka haifa ya amsa sunan jikan fari duka bangare biyu," 

Ranar suna yaro ya amshi suna Abdulmajeed mahaifin Dr jamal Ameena da kanta ta rada ma dan nata wannan sunan ansha shagalin suna an watse kowa ya koma gidansa lpy cike da farin ciki.

Majeed jikan fari yaro mai shiga rai kowa ya ganshi sai ya yaba da shi ya taso cikin soyayyar iyaye da kakanu baki daya.

Sai da majeed ya shekara 6 kafin matar yaya Aliyu ta sami juna biyu murna a wajen family 2 din nan baxai misaltuba. Bayan shekara daya suwaiba ta haifu ta haifi diyarta mace ranar suna aka sanya mata suna Amatullah taci sunan Hajiyar suby suna kiranta da Amal, " ansha shagalin suna sosai yayinda kowa yake cikin farin ciki Hajiya Hindu ta koma gidan Aliyu dan wankan jego ma yarta dan tace bamai yimata wankan jego sai ita Hajiya Amat maman suby tayi ta dariya tace to ki wanketa sosai kinsan mun samu kishiya Hajiya hindu tayi dariya kafin tace wannan aiba damuwa bane ko jikallena tana maganar tana kallon fiskar Amal dariya sukayi baki dayansu sannan sukaci gaba da hirarsu mai dadi.

Shekarar Amal 1 Hisham yayi aure ya auri kyakkyawar yarinya yar fulanin kasar Niger wacce suka hadu a Abuja taje gurin dangin babanta, " Hajiya hindu tace gwadamin hoton yar tawa kafin ta isona ganta Hisham yayi dariya kafin ya dauko wayarsa ya nuna mata pix din Amaryar tasa Hajiya hindu ta amshi wayan bakinta na furta masha Allah ashe wani jinkirin yakan zamo alkairi Allah ya baku xaman lpy da xuri'a daiyiba, " Hisham yadan sosa kai kafin yace Ameen Hajiyata murmushi Hajiya Hindu tayi kafinta mike ta nufi wajen bakinta......

Pls fans don't forget to read & share.
Love u much my fans

Taku har kullum Hauwa Ibrahim Misau 


Pls idan kunga akwai gyara ko yin wani abinda bai kamata ba ko bada shawara akan wani abu daya shafi rubuna pls ku nemeni ta wannan no din. 09039285813 .