MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Tara

"Murmushi Majeed yayi kafin yace dadina da kanka yana saurin kawo wuta da wuri, Daria Saleem yayi kafin yace ka kwantar da hankalinka kayi kusa komawa Nigeria baki daya, Majeed yace kwanaki kadan ya rage ma, haka sukaci gabada fira suna daria. Mommy ce zaune a falo tana kallo yayinda yan2 ke zaune a gefenta suna ta wasa kasancewa ranar juma'ane ba islamiya, Mee'ad ce ta fito daga dakinta jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta buga daurin kwalin da mata suke kiransa da TURE KAGA TSIYA! tayi kyau sosai ta fito ras abinta gwanin sha'awa,  ta karaso kujerar kusa da Mommy ta zauna tana cewa Mommy na shirya tsaf tin dazu,  Murmushi Mom tayi kafin tace yau sai gidan Hajiya kenan ? Mee'ad tace ai ina tinanin acan ma zan kwana,  Mommy tace Amal bata dawo ba har yanzu ko?'

MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Tara
          _*MEE'AD*_
                  
 
*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
 
Wattpad__@hauwancyy44
 
  
        JINJINA & SADAUKARWA
 
Na jinjina na kuma sadaukar da wannan littafin na gareki babbar aunty SAFNA ALIYU JAWABI Allah ya kara daukaka, basira da kuma fasaha ya kuma kareki da sharrin dukkan mai sharri. Ameeen .
                        
          19 ~ 20
Kwanci tashi ba wuya 'a wajen Allah yausu Mee'ad sun kammala secondary dinsu cikin farin cikin har sun fara shirye2 shiga jami'a, su Amal sai murna ake dan tana matukar son ta budi ido ta ganta a jami'a.
 
"Gama makarantar su Amal yayi dai2 da cika 4years din Yaya Majeed a India, yayinda soyayya tsakaninsa da Mee'ad take kara karfi fiye da tinanin mai tinani.
 
Mee'ad ce zaune bisa kujera a garden hannunta rike yake da wani novel na love story, karantawa take tana murmushi daga idon da zatayi tayi arba da Amal tsaye bisa kanta fuskarta dauke da murmushi ta janyo kujerar gefen Mee'ad ta zauna tana cewa 6 karatu ne ?"
 
"Murmushi Mee'ad tayi kafin tace eh! Amal ta gyada kai kafin tace naga 'alamar karatun nan yana miki dadi sosai, Mee'ad tace sosai ma kuma, shiru sukayi nadan mintuna kafin Mee'ad tace Bloody ya maganar Yayane kwana 2 shiru ko yar gaisuwan ma kin daina cewa yanayi min, yatsina fuska Amal tayi kafin tace ki daina damuna da zancen Majeed din nan dan Allah! 
 
Murmushi Mee'ad ta kuma yi kafin tace ai kuma Yaya yayi matukar damuwa dake fiyeda kowa 'a cikin gidan nan, Amal tace ni harna manta kamannin sama gaskiya kuma kinsan koda ya dawo gida ba'anan zai zauna ba  gidan Aunty zai koma, Mee'ad tace nasan da hakan amma barina fada miki yanzu Yaya ya zama hadadden guy kuma first class ga kyau ga ilimi ga kuma tarin son family a ransa sosai musamman ke", 
 
"Amal ta jawo kujerar da take kai cikin zumudi take fadin kikace kyakkyawan gaye ko ? Mee'ad tace kwarai ma kuwa !"
 
Amal ta kara gyara zama kafin taci gaba da cewa tinda ya zama kyakkyawa zan iya lallabawa nayi love dashi kodan kyawun da kika ce yana da, murmushi Mee'ad tayi kafin tace haba bloody dan kyau kuma ? Amal tace kwarai da gaske barima na shiga ciki na fara bama Umma labarin Yaya Majeed tana gama fadin haka ta nufi cikin gida cike da zumudi, binta da kallo Mee'ad tayi kafin ta girgiza kai ta ci gaba da karatun da take.
 
         %%%%%%%%%%%%%%
 
Yaya Majeed ne kwance bisa gado baki daya tinanin gida da Amal sun dami zuciyar sa, cikin tinani yaji kamar ana knocking kofar daki, ya dan gyara kwanciya kafin ya mike ya nufi bakin kofar, yana budewa yaga babban Abokin sane wato Saleem, yace yane guy ka shigo ciki mana Saleem ya shiga cikin room din yana daria, 
 
Saleem shine babban Abokin da Majeed yayi a India kasan cewar Saleem dan Nigeria ne kuma bahaushe dan uwan Majeed shiyasa jininsu ya jitu sosai ya kuma zama Babban Aboki a wajen Majeed din.
 
Zama yayi a kasa kafin yace Abokina  yau lfyanka kuma ? Murmushi Majeed yayi kafin yace mika gani a tattare dani wanda ya nuna maka banada lfy ? Daria Saleem yayi kafin yace malam maida wukan na gano matsalarka,  Majeed yace wannan kuma damuwar kace ba tawa ba Saleem ya gwalo ido kafin yace kaga malam banzo wajenka danka raina min wayo bafaah, ya tashi yana wani shan kamshi cewa yake ni kaga tafia tama Majeed yasha gaban Saleem yana cewa sorry Abokina na daina Allah, Saleem ya ce Allah idan ka sake bazan kara zuwa dakin kaba  Majeed yace naji kuma bazan sake din ba,"
 
Saleem ya bude freezer ya dauki lemo ya zauna bisa bed ya bude ya farasha yana kallon Majeed cewa yake nasan abinda ke damunka Abokina inaso ka kara kwantar da hankalinka kwana nawane ya ragema kwata2 ?"
 
"Yajaa dogon numfashi kafin yace Saleem bazaka ganeba nida kaina na janyo ma kaina, na zabi na zauna 'a kasar nan harna gama skull ba tare da naje gida ba Allah sai yanzu abin ke damina kanaga babu mai zuwamin visit saisu Dad da kuma Abba tin abin yana damina har ya daina, to kwana 2 din nan damuwan ya kara dawowa," 
 
Saleem ya mayar da darian dake shirin kubce masa kafin yace Abokina kace tinanin Kanwarka da son ganintane yaja maka kewar gida 'a dai2 wannan lokacin ko ?"
 
"Murmushi Majeed yayi kafin yace dadina da kanka yana saurin kawo wuta da wuri, Daria Saleem yayi kafin yace ka kwantar da hankalinka kayi kusa komawa Nigeria baki daya, Majeed yace kwanaki kadan ya rage ma, haka sukaci gabada fira suna daria.
 
Mommy ce zaune a falo tana kallo yayinda yan2 ke zaune a gefenta suna ta wasa kasancewa ranar juma'ane ba islamiya, Mee'ad ce ta fito daga dakinta jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta buga daurin kwalin da mata suke kiransa da TURE KAGA TSIYA! tayi kyau sosai ta fito ras abinta gwanin sha'awa,  ta karaso kujerar kusa da Mommy ta zauna tana cewa Mommy na shirya tsaf tin dazu,  Murmushi Mom tayi kafin tace yau sai gidan Hajiya kenan ? Mee'ad tace ai ina tinanin acan ma zan kwana,  Mommy tace Amal bata dawo ba har yanzu ko?'
 
" Tace eh! kafin taci gaba da fadin ina tsammanin acan itama zata kwana gaskiya, Mommy ta gyara zama kafin tace kice yau zakuyi mana yajin aiki kenan ? Murmushi tayi kafin tace kwarai ma kuwa, Mommy tace ba matsala Allah ya kiyaye hanya ki gaida Hajiyar, to tace kafin ta nufi bed dan dauko mayafi.
 
Mee'ad bata wani dade da tafiya ba Yaya majeed ya kira Mommy suka sha fira hadda yan2 anan yake shaida mata yayi kusa dawowa ya kamata su fara shirin karban bako, Daria Mom tayi kafin tace Allah ya dawo mana dakai lfy, aitin yanzu zan fara shiri har zuwa next year,yace yauwa Mommyta ki fara shirya min abubuwa da dama kinji ? Tace baka da matsala da wannan, Ya danyi shiru kafin yace ina yan matan gidan suka shigane ? Mommy tace Amal taje gidansu Ummanta ita kuma Mee'ad tana gidan Hajiya, Yace idansun dawo ki gaidasu mukwana lfy, nan sukayi sallama cike da kulawa da kuma kewar juna.....
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
MEE'AD FANS INA SANAR MUKU DA CEWA GOBE ASALIN LABARIN MEE'AD ZAI CIGABA, PLS KU BIYO NI KU SHA KARATU CIKIN JIN DADI FARIN CIKI HAR MA DA  WALWALA. 
 
Pls fans don't forget to read, vote & share to other groups.
Love u much my fans.
Taku har kullum Hauwancyy Misau <img data-emoji="