Matsalar Tsaro: Ya Zama Wajibi Malaman Addini A  Arewa Su Fito Su Baiwa Jonathan Haƙuri

Matsalar Tsaro: Ya Zama Wajibi Malaman Addini A  Arewa Su Fito Su Baiwa Jonathan Haƙuri

Daga Indabawa Aliyu Imam

Duk Malamin da ya hau Mumbari ya caccaki Jonathan a baya amma ya ƙi caccakar gwamnatin Buhari a yanzu Munafuki ne. Ba ranar da za ta fito ta faɗi ba a zubar da jinin bayin Allah a Arewacin ƙasar nan ba.

Ba mu zaɓi Buhari don wani dalili ba, sai don magance matsalar tsaro wanda ya sha alwashin aikatawa. Yau Buhari ya tafi shekara ta bakwai amma abubuwa sai lalacewa suke. 'Yan bindiga sun tare motar matafiya 25 sun ƙona su ƙurmus ba tare da laifin komai ba, akwai ƙananan yara da jarirai a cikinsu, amma kawo yanzu ba abin da gwamnati ta yi wa waɗannan tsinannu, sun kashe banza kenan.

Irin wannan ta'addanci ya faru fiye da lissafi a wurare daban-daban. A mulkin Buhari ne 'yan bindiga ke shiga ƙauye su kashe mutane dari uku ko ɗari biyu, su tafi kayansu sun kashe banza, haka gobe ma za su sake yi. A mulkin Buhari ne mutane ke mutuwa da yunwa saboda tsadar rayuwa da bakin talauci da gwamnatinsa ta kakaba wa al'umma.

A mulkin Buhari ne ake kashe 'yan Arewa a Kudu a sace musu dukiya ko a kona musu motoci amma gwamnati ko jaje ba ta yi balle d'aukan mataki. Yau duk wata gazawa da ke tare da Jonathan wancan lokacin Buhari yana da ita ninkin ba ninki. Amma malamanmu na Arewa da sarakunanmu sun yi shiru saboda kabilanci da son zuciya.

Mun gane masu hawa mumbari wancan lokacin suna koke-koke, tsine-tsine da alkunuti zafin talauci da kwadayi ne kawai ke damun su. Tun da bukatarsu ta biya yanzu a kashe duk wanda za a kashe ko a jikinsu.

Wallahi Malaman Arewa su sani su ababen tambaya ne kan shirun da suka yi ana yi wa al'umma kisan kiyashi. Kun kalubalanci Jonathan amma kun ƙi ƙalubalantar Buhari wanda za mu ce gwara Jonathan da shi sau dubu, saboda kwadayin abin da suke samu sun gwamnace kunyar lahira da ta duniya. Allah yana madakata kowa zai girbi abin da ya shuka.

Allah ya kawo mana agaji amma gwamnati ta gaza.