Mahara sun ɗauke mahaifiyar ɗan majalisa a Kano

Mahara sun ɗauke mahaifiyar ɗan majalisa a Kano

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun ɗauke mahaifiyar ɗan majalisar Kano, mai wakiltar Mazaɓar Ƙaramar Hukumar Gezawa, Alhaji Isyaku Ali Ɗanja.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na dare a jiya Talata a garin Gezawa, inda su ka karya kofar gidan su ka yi awon-gaba da ita.

Da ya ke bada bayanin yadda lamarin ya faru, Ɗanja ya ce ƴan bindigar sun nemi mahaifiyar ta sa da ta buɗe musu kofa amma sai ta ƙi buɗewa.

Ya ƙara da cewa da ta ƙi buɗewa, sai su ka karya ƙofar su ka tafi da ita.

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa bayan ƴan ta'addan sun bar gidan, sai ɗaya da ga cikin samarin da ke kula da mahaifiyar ta sa yai maza ya kira wani abokin siyasar ɗan majalisan yansahida masa.

"Tun kafin ma na je Gezawan, tuni Shugaban Caji-ofis na Gezawa ya kira ni a waya, ya shaida mini cewa tuni ma ya aike da jami'an sa zuwa wajen

"Ya gaya min cewa tuni ma sun fara bincike a kan lamarin.

"Sai dai kuma har yanzu maharan ba su tuntuɓe mu a kan ta ba. Mu na dai ta yin addu'a kan Allah Ya kuɓutar da ita lafiya," in ji shi.