Ma'ajin Jam'iyar PDP Ya Goyi Bayan Tafiyar  Mataimakin Gwamnan Sakkwato

Murtala Abdulkadir, ya fara da nuna farin ciki da jin dadinsa sosai ga wannan ziyara, ya gabatar da shawara, nasihohi kana ya jaddada goyon bayansa ga wannan kungiya, da yadda  za ta kara fadada ayukkanta na nemo hadin kan jama'a cikin birni da kauye domin kara samun nasara. Kamar yadda media team na kungiyar suka rubuta aka yada a kafar sada zumunta ta facebook.

Ma'ajin Jam'iyar PDP Ya Goyi Bayan Tafiyar  Mataimakin Gwamnan Sakkwato

Ma'ajin jam'iyar PDP na jihar Sakkwato Alhaji Murtala Abdulkadir Dan'iya ya bayyana sha'awarsa ga tafiyar mataimakin gwamnan jihar Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan'iya na tsayawa takarar gwamnan jihar a shekarar 2023.

Ma'ajin ya goyi bayan kungiyar WALIN SOKOTO ORGANIZATION FOR TRUST ( W-WOFT ) da aka kafa domin  bunkasa harkokin da za su samar da nasarori da Cigaban  Mataimakin Gwamna a lokacin da kungiyar ta ziyarce shi.

Murtala Abdulkadir, ya fara da nuna farin ciki da jin dadinsa sosai ga wannan ziyara, ya gabatar da shawara, nasihohi kana ya jaddada goyon bayansa ga wannan kungiya, da yadda  za ta kara fadada ayukkanta na nemo hadin kan jama'a cikin birni da kauye domin kara samun nasara. Kamar yadda media team na kungiyar suka rubuta aka yada a kafar sada zumunta ta facebook.
 
Shugaban kungiyar  Honarabul  Mika'ilu Abubakar Kofar Kade ya gabatar da Murna tare da  godiya zuwa ga Ma'aji bisa ga lokaci da karbuwa da kungiya ta samu a wurinsa. 
Haka zalika, ya kara da bayyana  makasudin ziyarar shi ne, ganin  jajircewar da Girman da Allah ya yi wa ma'aji  a cikin  Jiha da  Jam'iyar PDP ya sa suke rokon sa da yakasance Uba ga Kungiyar domin ba da shawara da za ta kara ba da nasara ga tafiyarsu.