Kwamishiya A Zamfara Ta Yi Murabus Domin Karɓar Muƙamin kwamishina Jihar Imo

Kwamishiya A Zamfara Ta Yi Murabus Domin Karɓar Muƙamin kwamishina Jihar Imo
Kwamishiniyar Mata da Yara ta Jihar Zamfara, Rabi Shinkafi ta yi murabus domin karɓar muƙamin kwamishina a Jihar Imo.
Da ta ke baiyanawa Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN, Shinkafi ta ce "Na yi murabus a matsayin Kwamishiniya a Zamfara domin karɓar wani muƙamin a Imo.
 "ina mai matuƙar godiya ga Gwamna Bello Matawalle da mai ɗakin sa, Hajiya A'isha Matawalle saboda alherin da su ke nuni da kuma bani damar yi wa Zamfara hidima a ɓangarori daban-daban.
"Duk wasu raɗe-raɗi da a ke yi a kan murabus dina ƙarya ne, aikin 'yan sharri ne.
Ni akwai kyakkyawar alaƙa tsakani na da gwamna da mai ɗakinsa.
"Da shi gwamnan Imo Hope Uzodinma da Matawalle sun tattauna a kan muƙamin nawa kuma dukkan su dai ƴan jam'iyar APC ne," in ji Shinkafi.
Wannan lamarin da ta yi yana da matuƙar ɗaure kai a ce mutum zai ajiye kujerar kwamishina ya tafi wata jiha ya karɓi kujerar kwamishina.
Abin da ta yi ya nuna akwai jihar da take zama a cikinta wadda ba 'yar asalin jihar ba ce kuma har a amince ta zama cikin majalisar zartarwar jihar.