Kungiyar PRO-Yari Group Ta Bada Tallafin Kayayyakin Agaji Ga Wadanda Hare-haren ‘Yan Bindiga Ya Shafa  A Zamfara

Kungiyar PRO-Yari Group Ta Bada Tallafin Kayayyakin Agaji Ga Wadanda Hare-haren ‘Yan Bindiga Ya Shafa  A Zamfara

 

 Daga  Aminu Abdullahi  Gusau.

 

A kalla yan gudun hijiriya 300 dake zaune a wata makaranta dake a karamar hukumar mulkin Anka dake jihar Zamfara   ne suka samu tallafin kayan abinci ta hannun wata kungiyar siyasa mai goyon bayan tsohon gwamnan jihar Zamfara Honorabul Abdul Aziz Yari Abubakar. 

 

 Kayayyakin da aka baiwa wadanda suka ci gajiyar wannan karimcin sun hada da, buhunan shinkafa, kayan sutura ga mata da yara.

 
 Da yake jawabi a lokacin rabon kayan agajin da aka gudanar a harabar makarantar da ke garin Anka, shugaban kungiyar, Mu’azu Yusuf Dangaladima ya ce  wannan mataki na daga cikin ayyukan jin kai da kungiyar ke yi ga wadanda ‘yan fashi da makami da sauran bala’o’i suka shafa a jihar.  
 
 A cewar Mu’azu Dangaladima, kungiyar ta bayar da irin wannan tallafi ga ‘yan gudun hijira da ke sansanin daban daban.
 

 "Mun yanke shawarar zuwa ne mu jajanta muku saboda abin da ya faru kwanan nan inda 'yan bindiga suka kashe mutane da dama tare da kone gidajen  wasu da dama daga cikin ku.
 
 “A  al’adar wannan kungiya, mun yanke shawarar kawo muku wannan karamcin ne da nufin rage wahalhalun da, da yawa daga cikin ku kuka samu kan ku a ciki, ” in ji shugaban.
 
 Shugaban kungiyar ya kuma jajanta a madadin  ‘yan kungiyarsa ga wadanda wannan bala’in ya rutsa da su, da kuma iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu.
 
 Ya kuma yi addu’ar Allah ya bai wa yan uwan  marigayan hakurin jurewa rashin,  ya kuma dawo da dawwamammen zaman lafiya a jihar Zamfara da ma Najeriya baki daya.
 
 A jawabinsa jim kadan bayan rabon kayayyakin, shugaban kwamitin masu kula da ‘yan gudun hijira na Masarautar Anka, Alhaji Aliyu Dan akalele wanda mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Anka, (Chiroman Anka) ya wakilta, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan karamcin da aka yi, sannan ya yi addu’ar Allah ya saka masa da membobin kungiyar sa da alheri.  

 
 "Zan iya tunawa a baya-bayan nan da kuka bayar da irin wadannan kayayyaki ga 'yan gudun hijirar a wannan masarauta, kuma a yau kun maimaita irin wannan abu, mun gode muku sosai".  Chiroman yace.
 
Wayanda suka halarci taron bayar da tallafin sun hada  da Kwamitin da ke kula da ‘yan gudun hijira na Masarautar Anka, da sauran masu biyayya ga tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari da suka hada da shugaban APC na bangaren sa, reshen  karamar hukumar Anka.

 
A wani bangare kuwa , mataimakin shugaban kungiyar  Alhaji Bello Ahmed, da Alhaji Bello Alin kilo Anka da Alhaji Bello Ahmed Rafin Gero ne suka jagoranci rabon kayayyakin, da  sauran jiga-jigan jam’iyyar a karamar hukumar mulkin Anka.