Kungiya A Gombe Ta Nemi A Karrama Tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha
A cewar sa Shekara 25 da bada jihar Gombe amma har yanzu babu wani waje na musamman da akq ware aka sanya sunan Marigayi Janar Sani Abacha, Inda yace a gaskiya Gombawa ba suyi kara ba. A dan haka sai ya yi kira ga Gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, da a samu wani waje kamar filin sauka da tashi na jiragen sama ko Asbitin kwararru ko jami'ar jihar Gombe ko Kuma a gina wani waje a sa sunan Marigayi Janar Sani Abacha Uban Gombawa. Kwamred Tanimu, yace idan akayi haka ya nunawa duniya cewa lailai Gombe sun karrama Uban su, amma a halin yanzu abun kunya ne ace duk girman jihar Gombe babu wani waje Mai sunan Marigayi Janar Sani Abacha bayan shi ya bada jiha.
Kungiya A Gombe Ta Nemi A Karrama Tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha
Daga Habu Rabeel, Gombe
Wata Kungiya Mai zaman kanta a jihar Gombe dake kokarin an daga sunan Marigayi Janar Sanu Abacha ta The Great founder of Gombe State Rememberance, tace bai kamata ace Gombawa sun manta Marigayi Abacha ba.