Kotu Ta Yi Ci Tarar Wani Saurayi Da Ya Yaudari Budurwarsa: Lauyoyi Na Neman Wanda Ya Ba Da Labarin  Na Ƙarya A Gombe

Kotu Ta Yi Ci Tarar Wani Saurayi Da Ya Yaudari Budurwarsa: Lauyoyi Na Neman Wanda Ya Ba Da Labarin  Na Ƙarya A Gombe

Daga Habu Rabeel Gombe

A 'yan kwanakin nan ne aka ga wani labari na yawo a kafafen sada zumunta na facebook da whatsapp kan cewa wata kotu majistare a garin Kumo taci tarar wani sauayi da ya yaudari Budurwar sa na kin auren ta tarar naira miliyan biyu da dubu dari shida bayan kuma babu labari makamancin haka.

Wannan rubutu da mai labarin mai suna Yusha’au Garba Shanga, ya jefa kan shi cikin matsala domin a halin yanzu Lauyoyi da Alkalai na neman sa dan jin inda ya samo wannan labari na ƙarya.

A wani taro da shugaban ƙungiyar lauyoyi na jihar Gombe Barista Ahmed Tukur da hadin guiwar bangaren Alkalai na kotun Majistare karkashin shugabancin Muhammad Tukur Jungudo, sun karyata labarin kuma sun sa a nemo wanda ya yi rubutun a duk inda yake.

A cewar kungiyoyin biyu wannan labari kwata-kwata kage ne babu shi kuma haka cin mutunci ne da bata suna wanda ba za su bari ba sai sun dauki matakin doka dan hakan ya zama darasi gamasu sha’awar irin wannan rubutu na batanci a kafafen sada zumun ta.

Rubutun an masa take ne kamar haka “WATA SABUWA:  Wata Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki Auren Budurwar sa” 

Ga rubutn da aka yi din Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi hukuncin taran N2.6m sakamakon yaudarar wata budurwar sa har na tsawon shekaru bakwai.

Budurwar ta yi ƙaran tsohon saurayin nata gaban kotun ne domin neman kotu ta bi mata haƙƙin ta tare da shaida mata cewa sun shafe shekara bakwai suna soyayya kwatsam sai ta samu labarin zai auri wata da ba ita ba.

Tuni alƙalin wannan kotu ya umarci wannan saurayi da ya biya ta zunzurutun kuɗi har N2.6m ko kuma ya aure ta ko ya tafi gidan gyaran hali na tsawon shekaru 8.

A bangaren saurayin, ya zabi ya fasa auran wacce akasa musu rana domin aurar tsohuwar budurwar sa da ta yi ƙarar sa.


Da yake Karin haske kan labarin shugaban kungiyar Alkalan kotunan Majistare din Muhammad Tukur Jungudo , cewa ya yi kotun majistare ba ta da hurumin sauraron kara kamar haka balle har ta yanke hukunci.

A cewar sa sun kira taron manema labarai ne dan su karyata wannan labara domin karya ne basu san wannan labarin ba, yin hakan bata suna ne kuma ba za su bari ba.

Daga nan sai yace sun sa a nemo wannan wanda ya yi rubutun dan ya gurfana gaban kuliya amma an ba’a same shi sai dai suna ci gaba da neman sa kuma duk inda ya shiga sai sun nemo shi domin ya bata musu suna, sai ya kara da cewa daga jin suna neman sa ya goge rubutun a shafin nasa bayan kuma jama’a sunyi ta yada shi.

 Labarin dai ya yi yawo sosai gami da hoton wata Yarinya dake nuna cewa ita ce budurwar, sai dai ba’afadi sunayen budurwar da saurayin ba haka ba inda aka ambaci dokar da aka dogara da ita wajen yin hukunci.