Kotu ta tura 'yar wasan Hausa Sadiya Haruna makarantar Islamiyya

Kotu ta tura 'yar wasan Hausa Sadiya Haruna makarantar Islamiyya
Kotu ta tura 'yar wasan Hausa Sadiya Haruna makarantar Islmiyya
 Kotu a hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yanke wa Sadiya Haruna hukuncin komawa makarantar Islamiyya ta Dharul Hadith na tsawon watanni shida. 
Da yake yanke hukuncin, Mai shari'a Ali Jibrin Ɗan zaki ya bayyana cewa Sadiya Haruna za ta dinga zuwa makarantar kullum tare da rakiyar jami'an hukumar Hisbah sannan za'a ajiye rijista ta dinga saka hannu duk ranar da taje. 
A satin daya gabata ne dai hukumar Hisbah ta Kama Sadiya Haruna inda aka zargeta da Saka hotuna da bidiyon batsa a kafafen sada zumunta.
Sadiya Haruna ta shahara a wurin harkar batsa da sunan tallar maganin ƙarfin maza ko na gyara sassan jikin mata.
Akwanan baya ta yi rigima da saurayinta wanda shima ɗan wasan Hausa ne in da ta ce sun yi auren mutu'a a tare da shi.
Bayan hatsaniya ta shiga tsakaninsu ne take faɗin ya yaudareta da wannan lamari.
Sai ga shi a yanzu Alƙali ya fahimci tana da ƙarancin ilmin addini akwai buƙatar ware mata wata shidda don samun ilmin addini.