Korona Ta Bulla A Fadar Shugaban Kasa Har Ta Kana Garba Shehu Da Wasu Mutum  Uku

Korona Ta Bulla A Fadar Shugaban Kasa Har Ta Kana Garba Shehu Da Wasu Mutum  Uku

Kafar yada labarai ta Premium Times ta rawaito cewa daga cikin wadanda suka kamu akwai Dogarin Shugaban Kasa, Yusuf Adado da babban mai tsaron Shugaban, Aliyu Musa da kuma kakakinsa, Malam Garba Shehu.

A bayanan da aka samu kwayar cutar ta kamamutane da dama a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Jaridar ta kuma rawaito cewa an gwada su ne tare da tabbatar da suna dauke da cutar a cikin makon nan.

Kazalika, rahoton ya kuma ce Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, na cikin wadanda suka kamun.

Rahoton, ya ambato Garba Shehu yana cewa, “Ba ni da tabbaci a kan abin da kuka fada, amma gaskiya ne, na kamu da samfurin COVID-19 ba mai tsanani ba.

“Ina jin dama-dama saboda an min rigakafi har hawa uku, garau nake jin kaina, yanzun nan ma na kammala motsa jikin da nake yi kullum na tsawon sa’a daya,” inji Garba Shehu.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da samfurin cutar na Omicron ke ci gaba da yaduwa a duniya.