Kisan Gilla A Arewacin Najeriya: Bayan 25 A Sokoto Sai Kuma Su Wa?

Kisan Gilla A Arewacin Najeriya: Bayan 25 A Sokoto Sai Kuma Su Wa?

 

Daga Comrade Yahaya M Abdullahi

 

Cikin alhini da damuwa ina miƙa ma 'yan uwana mutanen jihar Sokoto saƙon Ta'aziyya da kuma jaje tare da addu'a ta musamman ga waɗannan musulumai da aka zalunta, ace a kashe ka kuma a ƙona gawarka, amma fa ni ba irin saƙon jajen Shugaban Ƙasa Baba Manjo nake turowa ba, domin wani saƙon da ake sawa Garba Shehu ya mana dama ba'a yi ba sai ya fi Alkairi, amma ga wanda yake karantawa; ba ga masoyi makaho ba, ina nufin wanda yake son wannan Gwamnatin koda tayi laifi shi baya gani.

<spa n style="font-size: large;"> 

Haƙiƙa an yi asalin abunda ake kira da ta'addanci ko mu ce kisan Gilla a Sokoto, abun duk wani mutum mai mutunci lallai zai ji zafin lamarin, in ma shugaba ne  ba'a saƙon Allah-wadai kawai zai tsaya ba, lallai zai ɗauki mataki akan abunda ya faru.

 
An kashe mutane a baya kuma ana ta kashewa kullum, hanyoyinmu na Arewa yanzu in zamu hau su ba kuɗin Mota muke tunani ba, kuɗin fansa muke tunani, a baya in zaka yi tafiya ana maka tunanin haɗari ne amma yanzu tunanin 'yan Bindigar da za su bayyana su kashe ka ake yi, a saninmu da ɓarawo kuɗi yake karɓa amma wannan kuma rayuwa suke karɓa su wadanni irin Ɓarayi ne kenan?
 

A kullum za ka ji an kashe amma ba abunda yake canzawa, a wannan kam ma harda mace mai ciki ta Haihu da ita da Jaririn dukkansu sun zama toka, amma shiru kake ji, naso ace a kudancin Nijeriya ne hakan ta faru a nan ne za mu gane cewar lallai Gwamnati na aiki sosai domin mun ga hakan akan wannan yaron da 'yan uwansa Ɗalibai suka kashe shi ta hanyar tsafi, mu kuwa a Arewa a bayyane ake kashe mu, mun ma san saƙonmu daga farin gida, jaje ne kawai, dama za'a taimaka a daina mana jajen lallai sai yafi mana daɗi, mu san cewar mu a yanzu fa dabbobi ne kawai a ƙasar, rayuwarmu kawai ake bukata da dukiyoyinmu dake garuruwanmu.
 
'YAN AREWA INA MAFITA?
Mafita shi ne mu ce bamu yarda da wannan zaluncin ba, mu ce bamu amince ba, mu bamu san Ɓarawo da yake kashe mutane ba, to me yake bukata kenan?
Hakan na nuna a yanzu ba dukiyarmu ake bukata ba kenan ƙasarmu ake bukata, saboda in ba garuruwanmu ake so mu tashi domin a kwashe arzikin dake wajen ba me ya kawo kashe-kashe ba tare da wani dalili ba?
 

Ina Malaman Arewa da a kullum suke jikin manyan Gwamnati kuma su fito su zauna su ce za su mana wa'azin kwantar da hankali a Najeriya manyan ƙasar suna son mu? Na tabbata da a mulkin wani ne ba Ɗan Arewa ba da yanzu dukkan manyan Masallatai sun ayyana dokar yin alƙunuti domin a kori shugaban ƙasar, amma yanzu da yake nasu ne kuma iyayensu da yaransu ba su zuwa wajen ba su damu ba, mu mutu gaba ɗaya, a yi haƙuri kada ace na ci wa Malamai fuska domin sun san komai a ƙasar amma ba ita bace a gabansu su kawai in sun haɗu da manyan a ba su nasu ne kawai, amma fa wasu malaman ne gaskiya ke hakan kuma nasan an san su.
 
Zanga-zanga a Arewacin Najeriya an ce Haramun ne kada wani talaka ya fito zanga zanga haka Malaman suke faɗa mana, to don Allah shi kashe mu da ake yi ake yi, shiru Halas ne?
In ba Halas ba ne ka da ku hanamu Zanga-zangar lumanan nema ma kanmu mafita, in kuma ba haka ba shike nan, za mu fito cikin ƙanƙanin lokaci domin nuna damuwarmu akan halin da muke ciki a Arewa, wanda ya san shi mutum ne a Arewa Bismillah ya zo ya shiga cikin 'yan uwansa mutane domin Zanga-zangar neman 'yanci, domin neman 'yanci na mutane ne.
 
Allah ka kawo mana zaman lafiya a yankinmu na Arewa.

 
Comrade Yahaya M Abdullahi Ɗan Jarida, Marubuci za'a iya samunsa ta 07033800660.