Kawar Da Wahalar Aure Ne Maganin Matsalolin Tarbiya Da Ake Fama Da Su-----Shaikh Mustafa Sidi Attahiru

Kawar Da Wahalar Aure Ne Maganin Matsalolin Tarbiya Da Ake Fama Da Su-----Shaikh Mustafa Sidi Attahiru

Malamin addinin musulunci a jihar Sakkwato Shaikh Mustafa Sidi Attahiru ya bayyana cewa matsalolin da ake fama da su na lalacewar tarbiya yana da nasaba da wahalar aure da ake fama da ita a cikin aƙ'umma.
Malamin ya yi wannan kalamin ne a wurin taron Tasiri al'adu wajen tabbatar da zaman lafiya da ƙungiyar Sokoto Heritage Reloaded Initiative ta shirya domin samar da mafita ga al'umma.
Ya ce wahalar aure ne matsalar tarbiya domin samari na buƙatar aure amma tsadar lamurran auren ya hana su yinsa in da zina ta zama mai sauki a tsakaninsu.
"ƙarya da ake sanya wa tsakanin ma'aurata da uwayensu, ga kuma maganar al'adar kayan ɗaki da yin lefe da ke wahalar da kowane ɓangare a harkar aure, mi zai hana uwaye su ɗaukewa kansu wahalar yin kayan ɗaki, sai a mayar da sadaki ya koma matsayin kayan ɗakin ga wanda zai auri mace."
Malamin yana ganin kawar da al'ada ta wahalar da juna a lokacin aure shi ne kaɗai mafita ga gurɓacewar al'ada a cikin al'umma.