Jami'an Tsaron 'Civil Defence' Sun Fitar Da Sunayen Mutane 5000 Da Za'a Ɗauka Aiki

Jami'an Tsaron 'Civil Defence' Sun Fitar Da Sunayen Mutane 5000 Da Za'a Ɗauka Aiki
Hukumar tsaro ta 'Civil Defence' ta fitar da sunayen mutum 5000 da su ka samu nasara a ɗaukar aikin da za ta yi a 2022.
Aisha Rufai, Sakatariyar Hukumomin  'Civil Defence', Gidajen Gyaran Hali, da ta  Kula da Shige da Ficen Ƙasa ce ta baiyana haka a taron manema labarai a yau  Alhamis a  Abuja.
Ta ce hukumar ta kammala tsare-tsaren ɗaukar aikin na 2019, inda ta yi kira ga waɗanda su ka nemi aikin da su duba shafin ta na yanar gizo.
Ta ce waɗanda a ka tantance za su duba sunayen su a adreshin yanar gizo na http://cdfipb.carees da ga 17 ga watan Janairu domin samun ƙarin bayanai, inda ta ƙara da cewa sai waɗanda su ka samu nasara ne kawai za su iya buɗe shafin.
A cewar ta, shafin ba zai buɗewa waɗanda ba su samu nasara ba.
Ta ce a ranar 31 ga watan Janairu za a fara ɗaukar bayanai da karɓar takardun waɗanda a ka ɗauka aikin.
A nashi ɓangaren, Kwamanda-Janar na Hukumar, Ahmed Audi ya ce ɗaukar aikin tun na 2019 ne, in da ya ce bayan an gama tattara bayanai da takardun waɗanda a ka ɗauka aikin, sai kuma su shiga sansanin horo.