Ina kan tuntuɓar PDP da Gwamnoni da Ministoci kan takarar shugaban ƙasa da zan yi-----Gwamnan Bauchi

Ina kan tuntuɓar PDP da Gwamnoni da Ministoci kan takarar shugaban ƙasa da zan yi-----Gwamnan  Bauchi

Ina kan tuntuɓar PDP da Gwamnoni da Ministoci kan takarar shugaban ƙasa da zan yi-----Gwamna Bauchi

Gwamnan Bala Muhammad na Bauchi ya fara tuntuɓar abokansa gwamnoni da minista da shugabannin jam'iyar PDP a Bauchi kan ƙudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023.
Ya faɗi haka a ranar Jumu'a a lokacin da ƙungiyoyin matasa da direbobi suna nuna ra'ayin ya fito takara.
Ya ƙara da cewa iyalansa da abokansa da ya tuntuɓa sun ba shi goyon bayan ya yi takarar shugaban ƙasa.

Gwamnan Bauchi ya nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyarsu ta PDP abin da ake ganin wata barazana ce ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ganin yankinsu daya a Arewa maso Gabas kuma yana da karfi a jam'iyarsu ta PDP ganin shi dan siyasar gefen Jonathan ne..
Bala shi ma zai yi takarar kaman yanda gwamnonin da suka gabace suka yi in har bai samu tikitin takara ba ya dawo kan neman kujerarsa ta gwamna.