Ina Aka Kwana Kan Gidan Miliyan 700 Da Gwamnatin Sakkwato Ta Sayawa Majalisar Sarkin Musulmi?

Ina Aka Kwana Kan Gidan Miliyan 700 Da Gwamnatin Sakkwato Ta Sayawa Majalisar Sarkin Musulmi?

Jama’ar jihar Sakkwato a lokacin sun bayyana abin da gwamnatin jihar Sakkwato ta yi na sayawa majalisar sarkin musulmi gida da ofishi a birnin Abuja a matsayin babban kuskure da bukatar sake nazari da yin tunanin talakawan jihar, duk da bayanan da gwamnatin ta fitar a tabakin mai Magana da yawun gwamnan jiha Margayi Malam Imam Imam na cewa an bi ka’ida wurin sayen gidan, amma  mutanen jiha sun nuna rashin gamsuwarsu.

“Abin da ya sanya gwamnati ta  sayawa Sarkin Musulmi gidan miliyan 700 a Abuja wanda yake tare da duk wasu kayan da gida ke bukata da ofis saboda gwamnati ta fahimci akwai karancin ofis da wurin zama ga jami’an masarautar Sarkin musulmi sai aka sanya kudirin a cikin kasafin kudi na musamman na 2016 da kasafin kudi na 2017 miliyan 500 a sayi gida, miliyan 200 a sayi ofis, majalisar zartarwa ta jiha ta aminta da hakan” a cewar Margayi Imam

Malam Imam Ya yi wadan nan kalamai ne bayan hukumar EFCC ta gayyaci Sarkin Fadan Sakkwato Alhaji Kabiru Tafida ta yi masa tambayoyi a Talata da Larabar data gabata, ta bayar da shi beli bayan ta samu bayanin miliyan 700 da ta samu acikin asusun ajiyarsa daga gwamnatin Sakkwato suke suna da alaka da Sarkin Musulmi.

Malam Aminu Muhammad ya ce “Gwamnatin Sakkwato tana kokarin kare kanta ne ga zargin, da samar da  lamarin da take kokarin kare kanta ga wasu takardu da ta bayyana suma suna da alamar tambaya ga wanda zai dauke su madogara. A wurina ko nawa aka ce an ware a saya Sarkin Musulmi gida da zai samar da nutsuwa a garesa ya dace a matsayinsa na jagoran musulmin kasar nan, gidan miliyan 500 ya yi kadan ga Sarkin musulmi a lokacin da shugabannin siyasa da gwamnoni da sanatoci da sauransu suka mallaki na biliyoyin kudi ba zaka iya lissafa ‘yan siyasar dake da gidajen biliyoyin kudi a Abuja ba.

Sai dai ba nan gizo ke saka ba wane tsari ne gwamnatin ta bi na fitar da kudin da har ya janyo hankalin EFCC, na yarda an yi Memo an yarda da shi a majalisar zartarwa, abin tambaya anan an bi ka’ida wurin fitar da kudin don takardun da nagani ba wata sadarwa a ma’aikatar kudi wadda ita ce ke da alhakin fitar da kudin, miyasa aka ajiye kudin a asusun mutum daya, ba a kai asusun masarauta ba ko hukumar gidaje ta kasa, M/S da FAWAD an ba su kwangila ne?” a cewar Aminu.

Ya kara da fadin ‘wannan harkalla ta bayyana yadda gwamnati ke satar kudin jama’a a kowace rana amma suna fadawa talakawa matsin tattalin arziki ya hana a yi masu aiyukkan cigaba.

Masu kula da harkokin yada labarum gwamnati a kokarinsu na yadda lamarin zai mutu ya bar baya da kura don ba su yi karatun ta natsu ba kafin yada lamarin ga kafafen labaru a kokarin sanya wa lamarin ruwa suka sanya wa wutar fetur sun rage kimar gwamnati a idon jama’a, mutanen Sakkwato na son sanin shin an saye gidan, a ina aka saye shi kuma ga waye, tun yaushe aka fitar da kudin, mi kudin ke yi a asusun mutum daya kuma ana nufin aikin jama’a da su.’ in ji Aminu Muhammad.

Wani da aka sakaya sunansa  ya ce yunkurin yana da kyau amma an yi shi ba cikin lokacin da yadace ba, Sarkin musulmi ana samar masa gida duk in da yake so kuskuren da aka yi tura kudi a asusun mutum daya babban kuskure ne shi zai nuna wannan almundahana ce da gwamnati ke yi an so a kwashe kudin ne labawa ne aka yi da shi don an san ana ganin girmansa da kimarsa tun da asiri ya tonu.

Sadiya Nasir ta ce ‘shin abin tambaya anan Sarkin musulmi na bukatar gida a Abuja ne wane irin abu ne sarkin musulmi zai yin na sirri wanda ba zai iya amfani da masaukin baki na shugaban kasa ba ko na gwamnatin Sakkwato ko na majalisar koli na harkokin addinin musulunci ko na jama’atu Nasril Islam.

Ya za a ce an fitar da wannan kudin a saya Sarkin Musulmi gida a lokacin da jama’ar jihar Sakkwato da ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu a Karamar hukumar Ilela da Sabon Birni da Gada da Silame da Dange Shhuni da  Kware ke cikin wahala da neman wurin zama da abinci, su ba ma son su samu na kwarai ba wanda ma za su zauna suke so, ka tafi makarantunmu ka ga yanda yara suke zaune a kasa ba kujerin zama wasu wuraren ma ajujuwan sun kware, an fara jarabawar canjin aji a makaratunmu amma an kasa raba masu takardun tambayoyi sai dai malami ya rubuta da allo da sauran abubuwa birjik amma gwamnati ta fitar da wannan kudin miliyan 700 don wata bukata ta daidaikun jama’a ta kyale talakawa wannan babban kuskure ne’ a cewar Sadiya.         

 Managarciya ta fahimci a yanzu sama da shekara hudu kenan da sayen gidan duk da bukatar da mutane suke  da ita na sake nazari kan sayen gidan da gwamnatin jiha ta yi amma ba ta waiwayi lamarin ba, kusan ana iya cewa lamarin an ci an canye kenan tun da gwamnati ta gamsu da abin da ta aiwatar.