Hukumar Zaɓe Ta Tura Ma'aikata Dubu 12 Don Gudanar Da Zaɓen Abuja

Hukumar Zaɓe Ta Tura Ma'aikata Dubu 12 Don Gudanar Da Zaɓen Abuja

Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ce za ta tura ma'aikatanta dubu 12 don gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin Abuja a 12 ga watan Fabarairu.

Kwamishinan zaɓen Abuja Alhaji Yahaya Bello ya sanar da hakan a Laraba wurin taron masu ruwa da tsaki da ƙungiyoyin sa kai.

Hukumar ta tabbatar da yin adalci a tsakanin 'yan takara a lokacin zaɓe.

Ya yi kira ga ƙungiyoyin mata su fito don wayar da kan 'yan ueansu ga yin zaɓen wanda suka cancanta.