Haɗin Nama Da Shinkafa A Cikin Ƙwai Girkin Da Bai Taɓa Gundurar Magidanta

Haɗin Nama Da Shinkafa A Cikin Ƙwai Girkin Da Bai Taɓa Gundurar  Magidanta

BASAKKWACE'Z KITCHEN

Haɗin Nama Da Shinkafa A Cikin Ƙwai Girkin Da Bai Taɓa Gagarar Mai Cinsa

MEAT & RICE IN EGG


INGREDIENTS
 Shinkafa
 kwai
nama
 peas & carrot
albasa da lawashi
attaruhu da tattasai
oil or maggrine
tafarnuwa
maggi da gishiri thyme
 
METHOD
Da farko za ki  sami markaɗɗaɗen naman ki, ki zuba a tukunya.
Ki samu curry, tafarnuwa,lawashi,thyme,maggi da gishiri ki zuba ki juya sannan ki barshi ya dahu.
Sannan ki wanke shinkafa kiyi mata rabin dahuwa Sannan ki kara wanke ta, ki tsame ta da matsami Sai kuma ki ɗaukko wannan naman ki zuba a kasko mai faɗi ki zuba mai ko margin ki soya sama-sama Sannan ki ɗaukko shinkafar ki, ki zuba akai sai ki sami attaruhu ko tattasai ki jajjaga ki zuba akai ki juya Sai ki samu carrot da peas ki goge bayan carrot din ki yayyanka Sai ki zuba ruwa ki juya sosai Sai ki barshi zuwa 'yan mintuna Sannan ki sami ƙwai ki fasa akai ki juya sosai Sai ki barshi ya dan dahu Sannan ki sauke sai ki wanke hannu ko cokali ki hau ci.

Wannan haɗi yana matuƙar burge magidanta musamman waɗamda suka taɓa cinsa sukan yi santin cigaba da samun irin wannan haɗin.

Magidanta da ba su taɓa cin irin wannan ba akwai tsananin buƙatar matansu, su burge su da kalar wannan haɗin da ake kira shafe laifinki ga mai gida.


MRSBASAKKWACE