Gwamnoni Sun Ba Da Gudunmuwar Miliyan 50 Ga Iyalan Mutanen Da Mahara Suka Ƙone a Sakkwato

Gwamnoni Sun Ba Da Gudunmuwar Miliyan 50 Ga Iyalan Mutanen Da Mahara Suka Ƙone a Sakkwato

Gwamnoni Sun Ba Da Gudunmuwar Miliyan 50 Ga Iyalan Mutanen Da Mahara Suka Ƙone a Sakkwato

Ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma ta bayar da gudunmuwar miliyan 50 ga iyalan mutane 23 da 'yan bindiga suka ƙone a ƙaramar hukumar Sabon Birni dake jihar Sakkwato.
Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ne ya gabatar da takardar Cek ta kuɗin ga Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal domin a miƙa kuɗin ga iyalan a yau Laraba zauren fadar gwamnatin jiha.
Yankin ya ƙunshi jihohin Sakkwato da Zamfara da Jigawa da Kaduna da Kano da Kebbi da kuma Katsina.
Tambuwal ya yi alƙawalin miƙa kuɗin ga iyalan margayan da 'yan bindigar suka ƙone a cikin mota a satin da ya gabata