Gwamna Matawalle Ya Ziyarci Sojojin Da Suka Ji Rauni A Fagen Daga 

Gwamna Matawalle Ya Ziyarci Sojojin Da Suka Ji Rauni A Fagen Daga 
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ziyarci sojojin da su ka samu raunuka a yaƙin da su ke yi da ƴan ta'adda a yau Asabar.
Gwamna Matawalle ya ziyarci sojojin ne a asibiti, sanye da kayan sojoji da rigar tare harsashi.
Bayan ya musu fatan samun sauƙi, gwamnan ya jaddada ƙudurin gwamnatin sa na tallafa musu da kula da lafiyar su.
A jiya ne dai rahotanni su ka baiyana cewa ƴan ta'adda masu fashin daji sun hallaka sama da mutane 150 kuma da dama sun ɓata a wani hari da su ka kai kan wasu ƙauyuka a Zamfara.