Gwamna Ganduje ya naɗa sabon sarkin Gaya

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin  Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da naɗin Alhaji Aliyu Ibrahim a matsayin sabon sarkin Gaya,

Gwamna Ganduje ya naɗa sabon sarkin Gaya
Gwamna Ganduje ya naɗa sabon sarkin Gaya

Gwamna Ganduje ya naɗa sabon sarkin Gaya

Daga Ibrahim Kano

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin  Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da naɗin Alhaji Aliyu Ibrahim a matsayin sabon sarkin Gaya,

Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da hakan a cikin daren jiya Asabar a gidan gwamnatin Kano.

Sakataren gwamnatin ya ce, sahale naɗin nasa ya faru ne sakamakon shawarar sunaye uku da masu naɗin sarki a masarautar suka gabatar.

Hakan nan ya kara da cewa bayan tantance mutanen ne gwamnati ta amince da naɗa Alhaji Aliyu Ibrahim a matsayin sabon sarkin.

Alhaji Aliyu Ibrahim, shi ne babban ɗa ga marigayi sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulƙadir, kuma kafin bayyana sunansa a matsayin Sarkin na Gaya mai daraja ta ɗaya yana rike da mukamin Chiroman Gaya.

In dai ba'a manta ba a ranar  Laraba 22  ga watan Satumba da muke ciki ne ne dai Sarki Gaya ya rasu wanda yana daya daga cikin sabbin sarakunan 4 da gwamna Ganduje ya kirkira.