Gidauniyar Ambasada Rufai Danmaje Ta Yaye DalibaI 10,500 A Kano

Ya kara da cewa, matasa na da rawar takawa wajen bunkasa tattalin arzikin arewa, don haka ya yi kira masu karfi da ke cikin al'umma da su jawo su a jiki su tafi tare da su. ya kuma yi kira da ƴan kasuwa da shugabanni da ma masu hannu da shuni da su rinka taimakawa rayuwar matasa domin samun habaƙa tattalin arzikin arewa da  kasarmu Nigeriya, sannan ya yi albashir cewa, nan da watanni kadan cibiyar ta sa za ta yaye mutum 3500 akan fannoni daban-daban. Daliban, da suka fito daga kananan hukumomi 44, sun koyi Diploma ta kwararru akan aikin Jarida, kiwon kifi daukar hoto, Ɗinki, P.O.S, Walda, gyaran waya.Noman rani da sauransu.

Gidauniyar Ambasada Rufai Danmaje Ta Yaye DalibaI 10,500 A Kano

 

Daga Ibrahim Hamisu, Kano,

 

Gidauniyar Ambasada Rufa'i Danmaje ta yaye dalibai 10,500 a bangarorin Ilimi  daban-daban da ya gudana a gidan Mumbayya da ke Kano a ranar Talatar da ta gabata.

 

Gidauniyar wacce Ambasada (Dr.) Rufa'i Mukhtar Danmaje ke jagoranta, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar da suka da mu da cigaban Arewa wato Arewa Concern Citizens For Development ACCD, kuma shi ne Sarkin samarin Arewa, ya godewa Allah da ya ba shi ikon daukar nauyin wadannan dalibai maza da mata.

Ya kara da cewa, matasa na da rawar takawa wajen bunkasa tattalin arzikin arewa, don haka ya yi kira masu karfi da ke cikin al'umma da su jawo su a jiki su tafi tare da su. ya kuma yi kira da ƴan kasuwa da shugabanni da ma masu hannu da shuni da su rinka taimakawa rayuwar matasa domin samun habaƙa tattalin arzikin arewa da  kasarmu Nigeriya, sannan ya yi albashir cewa, nan da watanni kadan cibiyar ta sa za ta yaye mutum 3500 akan fannoni daban-daban.
 
Daliban, da suka fito daga kananan hukumomi 44, sun koyi Diploma ta kwararru akan aikin Jarida, kiwon kifi daukar hoto, Ɗinki, P.O.S, Walda, gyaran waya.Noman rani da sauransu.
 
Da ma dai wannan ba shi ne karo na farko ba da wannan gidauniya ke tallafawa mata da matasa ba, kamar koyar da sana'o'i tallafin asibiti tallafin karatu da sauran ayyukan cigaban al'umma,
 
Malam Sharu Kwaru da Mal. Adamu Chiroma Kwaru da A'isha Abubakar sun bayyana jindadinsu da nasarar da sukai wajen samun wannan tallafi na sana'ar Noma da kiwon kifi da sukai,
 

Taron dai ya samu halartar manyan baki da suka hada da: Haj. Bilkisu Mahe Bashir Wali babbar Jami'a daga Babban Banki Kasa wato CBN, Kwamishinan na Ayyuka na Musamman Hon. Mukhtar Ishaq Yakasai, Dr. Nasir Tijjani daga asibitin kashi na  Dala, Imam Mahi Naniya, Dr. Sheikh Mujaheed Aminudeen Abubakar da  kungiyoyin cigaban al'umma irinsu Mu hadu Mugyara da kuma ƙungiyar tsaro ta Fagge.