Game Damu

Kamfanin DMM Publication and Media Service Limited, dake buga Mujallar Managarciya. Kafar sadarwa ce mai mazauni a jihar Sakkwato da manufar amfani da ƙarfin alƙalami wajen gano rawar da mata ke takawa da kuma gudunmuwar da suke bayarwa a cikin al’umma a fannoninin rayuwa da tattalin arziki da kuma siyasa, su ne ƙashin bayan fito da wannan mujalla mai suna MANAGARCIYA. Mujallar ba za ta yi ƙasa guiwa ba, wajen zaƙulo maku muhimman bayanai da suka shafi ƙasa da Duniya, akwai maƙalolin masana harshen Hausa da labarai da tattaunawa da mutane daban-daban kan lamurran ƙasa da rayuwar al’umma don samun ci-gaba maiɗorewa.

Mai karatu ka sani yabawa da gyarawa da kuma tallafawa rawar da mata ke takawa da ƙarfafa shigar su a fagen al’amarin rayuwa, tattalin arziki da siyasa ta hanyar la’akari da addini da al’adun jama’a ne ya sanya mu fito da wannan mujalla da za mu ba da ta mu gudunmuwa a gina al’umma abin alfahari ga kowa.

Duk wanda ke da wata gudunmuwa ƙofar mu a buɗe ta ke domin haɗa kai ga samun nasarar gina al’umma ta-gari.
Managarciya an ƙirƙiro ta ne a 2018 da zimmar yabawa da kuma tallafawa rawar da mata ke takawa don a kara ƙarfafa shigarsu a fagen rayuwa.

Mun tsunduma ne domin taimakawa ƙasa a ilmantar a fadakar da al’umma lungu da saƙo domin zaburar da a cigaban rayuwa, daidai yanda doka da ƙwarewa a aikin jarida ya tanadar.

Muna buga Managarciya a online, muna kuma fitar da kwafinta domin sayarwa jama’a a wurin masu sayar da jaridu a Nijeriya gaba ɗaya.

Ma’aikatan Managarciya

Ma’aikatan Managarciya

Dakta Kulu Abubakar mfr,: Babbar Edita/Darktan gudanarwa.

Muhammad Muhammad Nasir: Editan Zartarwa

Akilu Shehu Yabo, Mustafa Ahmad: Mataimakan Edita

Bello Sambo Bazza: Mai tallafawa Edita

Basit Ahmad, M. A Faruk: Editan Shafuka

Sadiya Attahiru Jabo: Mai kula da yanar gizo

Masu bayar da gudunmuwa

Farfesa Sa’adiya Omar

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai

Dakta Aisha Balarabe Bawa

Dakta Balkisu Sa’idu

Dakta Umar Bunza

Malam Usman Buhari Sani

Umar Bandi Kofar Kware

Nafisa Kabiru Muhammad

Saratu Zubairu

Aisha Bashir

Aisha Nana Alhassan

Fatima Lawal Safiya Usman

Jami’in kula da kasuwanci

Muhammad M. Nasir

Editan hoto

Murtala Abubakar ST

Lauyan kamfani

Barista Safiyya Muhammad