El-Rufa’i Zai Rabawa Talakawan Jihar Kaduna Tallafin Naira Biliyan Hudu Domin Rage Radadin Talauci

El-Rufa’i Zai Rabawa Talakawan Jihar Kaduna Tallafin Naira Biliyan Hudu Domin Rage Radadin Talauci

El-Rufa’i Zai Rabawa Talakawan Jihar Kaduna Tallafin Naira Biliyan Hudu Domin Rage Radadin Talauci

Gwamnatin jihar Kaduna ta ware Naira Biliyan hudu da zata rarrabawa talakawa a duka kananan hukumomi 23 dake fadin jihar a shirinta na tallafawa mararsa karfi domin su dogara da kansu.

Bayanin hakan ya fito ne daga Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), a yayin ganawarsa da yan Jaridar a Ofishinsa.

Kwamishinan yace shirin tallafin zai bawa Gwamnati damar jin kan jama’a kai tsaye musamman mazauna karkara.

RARIYA ta ruwaito Dattijo yace Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai nada azamar ganin jama’a sun samu rayuwa cikin wadata da walwala shi yasa ya kagu wajen ganin an ninka kudaden tallafin ya haura Biliyan N24 a shekara mai zuwa.

Za a rabar da kudaden ne a karkashin shirin rage radadin talauci da Gwamnatin jihar Kaduna ta kirkiro kuma zata kaddamar a sabuwar shekara.