Direba Ya Rasa Ransa A Cikin Tankar Man Fetur A Kano

Direba Ya Rasa Ransa A Cikin Tankar Man Fetur A Kano

 

Direban babbar mota Dahiru Aliyu Hotoro mai shekara 45 ya rasa ransa a cikn tankar Man fetur kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar.

 Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, shi ne ya fitar da sanarwar faruwar lamarin a ranar Talata, amma lamarin ya faru ne a ranar litinin data gabata kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Hukumar ta ce ta samu kiran waya ne ta hannun wani Shu'aibu Muhammad da safiyar ranar, a take suka tafi in da abin ya faru da misalin karfe 10:59 suka tarar direnan ya bar duniya.

Ya kara da cewa, Aliyu ya shiga cikin tankin motar ne domin wanke man da ke ciki, amma aka yi rashin sa’a ya makale a ciki har ya mutu ya kasa fita sai bayan rasuwarsa aka fahimci yana ciki bai fito ba.

Rayuwa kenan kowa da in da Allah yake kaddari ya rasa ransa da hali da kuma yanayi, wannan direban ya rasa ransa a wurin da yake neman abincinsa.