Buhari:Abin Da Ya Sanya Ban Sanyawa Dokar Zaben Kato Bayan Kato Hannu Ba

Buhari:Abin Da Ya Sanya Ban Sanyawa Dokar Zaben Kato Bayan Kato Hannu Ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilansa na kin rattabawa dokar zabe da aka yi wa gyaran fuska hannu wadda ke tare da maganar zaben kato bayan kato ya zama cilas a jam'iyyun siyasa na Nijeriya.

 Shugaba Buhari ya rubuta wasika ga shugaban majaliasar dattawa Ahmad Lawan dalilansa na kin sanya hannu ga daftarin dokar zabe na 2021.

Buhari ya ce halin da kasar Nijeriya take ne ya hana masa sanya hannu ga daftarin ga kuma kashe kudi sosai ga lamarin zaben kai tsaye waton kato bayan kato.
Ya cigaba da cewa ga kalubalen tsaro a wurin sanya idanu a zaben, ga kuma take hakkin 'yan kasa in da za a yi wa kananan jam'iyyu babakere da sauran abubuwa su ne suka sanya shi yaki sanya hannu.
Buhari ya ce samun shawarwari ne a wurin hukumomi da ma'aikatun gwamnati hakan ya sanya ya natsu ya duba daftarin ya gwamaya shi ga halin da ake ciki ya fahimci komi na iya faruwa.
Shugaba Buhari ya ce abin da yafi dacewa a bari kowace jam'iya ta yi zaben fitar da 'yan takararta yanda take so.
Buhari ya bayar da wannan bayanin ne bayan kwanakin da doka ta bashi na sanya hannu ya kammala waton kwana 30.