Buhari Ya Bayar Da Umarnin Fatattakar 'Ƴan Bindigar Da Ke Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Buhari Ya Bayar Da Umarnin Fatattakar 'Ƴan Bindigar Da Ke Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin fatattakar ƴan bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma na wasu sassan ƙasar.

Jaridar Daily Trust a Najeriyar ta ruwaito ministan harkokin cikin gida na ƙasar Rauf Aregbesola yana sanar da hakan a yau Alhamis bayan taron majalisar tsaro ta tarayya wanda shugaban ƙasar ya jagoranta a fadarsa.

Ya bayyana cewa shugaban ya ba dukkannin jami'an tsaron ƙasar umarni da kada su yi ƙasa a gwiwa su tabbatar sun kawar da duk wasu ɓarayi da masu garkuwa da mutane da duk wasu nau'uka na laifuka.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna dai ta zama tamkar tarkon mutuwa ganin yadda ake yawan samun ƴan bindigan na yi wa matafiya kwantar ɓauna.

Ko a makon nan sai da ƴan bindigan suka sace gwamman mutane da kuma kashe wani fitaccen ɗan siyasa a Najeriyar.