Bayan Shekaru 14 Fati Muhammad Ta Dawo Wasan Hausa

Bayan Shekaru 14 Fati Muhammad Ta Dawo Wasan Hausa

 

Sananniyar jarumar finafinan Hausa, Fati Muhammad ta dawo Kannywood, bayan shafe shekaru goma sha huɗu da daina sana’ar wasan Hausa.

 

Dawowar Fati ta samu fatan alheri daga masoyanta da masoyan finafinan Hausa, bayan dogon lokaci basa ganinta.

 
Ta dawo hharkar  a matsayin mai shiryawa  kamar yadda wata gajeriyar sanarwa ta bayyana a shafin Facebook na ‘Kannywoodcelebrities'.
 
A ranar Talatar nan dai sabbin hotunan jarumar suka karaɗe shafukan Sada Zumunta, musamman Facebook da instagram, wanda hakan ke nuni da cewa al’umma suna farin ciki da dawowarta harkar finafinan Hausa, duk da harkar na neman durkushewa.
 
A cikin hotunan, a kwai wanda a ka nuno  Fatin a zaune kan wata kujera yayin da ake ɗaukar wani sabon fim, wanda za ta taka rawa a cikin sa.
 
A na tunanin cewa wannan shi ne shiri na farko bayan dawowarta harkar fina-finan Hausa.
 
Fati, 'yar asalin Jihar Adamawa, ta fara harkar fim tun tana ƙarama har zuwa yanzu da girma ya zo.
 
Fina-finanta da su ka yi fice sun hada da Sangaya, Zarge, Marainiya, Mujadala, Kudiri, Tutar So, Garwashi, Tawakkali, Gasa, Abadan Da’iman, Zo mu Zauna, Tangarda, Hujja, Al’ajabi, Halacci, Samodara, Zumunci, Murmushin Alkawari, Gimbiya, Bakandamiya, Taskar Rayuwa, Babban Gari, Tsumagiya da dai sauransu.
Dawowar Fati ya zo da mamaki ganin yanda ta shafe lokaci a waje amma ta fita batun fita a finafinnai sai kwatsam aka ji ta dawo ruwa.