Ban Yi Tsammanin Bayan Na Bar Mulki Mutanen Nijeriya Su Yaba Min Ba----Shugaba Buhari

Ban Yi Tsammanin Bayan Na Bar Mulki Mutanen Nijeriya Su Yaba Min Ba----Shugaba Buhari

 

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce shi dama ba ya tsammanin mutanen  Nijeriya za su yaba masa bayan ya bar mulkin kasa.

 

Buhari ya bayyana hakan ne a hirarsa ta musamman da ya yi da gidan talabijin na ƙasa, waton NTA.

 
Buhari ya ce shekara da shekaru ya na riƙe madafun iko a ɓangarori daban-daban a ƙasar nan kuma ya ba da iya gudunmawar da zai iya bayarwa.
 
"Me zan yi sama da abin da na yi wa ƙasar nan?"
 
Ya ƙara da cewa ya na fatan idan ya kammala mulkinsa a 2023, 'yan Nijeriya za su gane cewa ya yi iya iyawar sa kan lamurran kasa.
 
"Na yi gwamna, na yi minista kuma gani a karo na biyu a matsayin shugaban ƙasa. Sabo da haka an dama da ni a harkar mulki. To, me kuka zan yi sama da wannan?," a cewar Buhari.
 
"Na yi iya kokari na kuma ina fatan bayan na bar mulki, 'yan Nijeriya za su yi duba na tsanaki. Ni ba na tsammanin wani yabo, amma abin da na ke tsammani shi ne 'yan Nijeriya za su ce mutumin nan ya yi iyakar ƙoƙarinsa. Ni wannan na ke tsammani da ga mutanen  Nijeriya," in ji Buhari.
Manazarta na ganin wannan bayanin nasa nada nasaba da yanda ya samu bayanin tabarbarewar abubuwa masu yaka tun a gefen tsaro da tattalin arziki, ga yanda lamurran rashawa suka karu wannan abin dubuwa ne a wurin sa da yin tsammanin in aka samu canjin lamurran fiye da yanda ake kan mulkinsa mutane ba za su yaba masa.
Mutanen Nijeriya sun zabi Buhari ne domin a samu sauyi kan lamurran tattalin arziki da tsaro, ga shi a yanzu ba a wani abin masarufi da bai ninka kudinsa sau biyu ba, tsadar rayuwa ta karu a tsakanin talakan kasar Nijeriya.