Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Biyu

Tun 5am na tashi na shiga kitchin na ɗaura mana lafiyayyen break fast sannan na je na yi salla , ina fitowa na koma kitchin ɗin. Har lokacin bacci suke yi yayinda ni kuwa ajima_ajima saina shiga ɗaki na duba ya suke? sunanan kuwa?.     Sai 8am sannan suka fito su dukansu na gabatar masu da kayan break fast ɗin , sosai suka ci abincin hakan kuwa ba ƙaramin faranta min tai ya yi ba.   Ƙarfe 9am su Baba suka fita domin zuwa ofishin jami'an tsaro don ganin waƴanda aka kama da kuma jin idan akwai ragowarsu , su daiji mai dame za'ayi yanzu kamin case ɗin yakai kotu.

Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Biyu
BABBAN BURI
 
 
 
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
 
 
 
 
SADAUƘARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI. {SHATU}.
 
 
 
 
 
FITOWA TA ISHIRIN DA BIYU
 
 
 
 
~~~ A wannan daren munyi farin ciki marar misaltuwa na bayyanar su Umar, cike da murna na yi masu wanka na wanke su fess, sannan Hajiya Inna ta kawo masu tuwon shinkafa fara soll da'ita da miyar kuka wacce ta ji man shanu , nan suka hau cin abinci hannu baka hannu ƙwarya.
 
Mama kam ba bakin magana , sai dai tana ta biyan mu da idanuwa tana murmusawa.
 
A wannan daren komi zaman bacci ɓarawo a haka ya barni domin kuwa ina tsoron a koma ɗauke mana ƴan uwa, duk da Ya Haidar ya sanar mana an samu nasarar damƙe su , kotu yanzu za'a tura case ɗin.
 
A haka kowa yana baccinsa ni kuwa na sanya su gaba ina kallonsu suna bacci cikin kwanciyar hankali.
 
 
*Washe gari.*
 
Tun 5am na tashi na shiga kitchin na ɗaura mana lafiyayyen break fast sannan na je na yi salla , ina fitowa na koma kitchin ɗin.
Har lokacin bacci suke yi yayinda ni kuwa ajima_ajima saina shiga ɗaki na duba ya suke? sunanan kuwa?.
 
 
Sai 8am sannan suka fito su dukansu na gabatar masu da kayan break fast ɗin , sosai suka ci abincin hakan kuwa ba ƙaramin faranta min tai ya yi ba.
 
Ƙarfe 9am su Baba suka fita domin zuwa ofishin jami'an tsaro don ganin waƴanda aka kama da kuma jin idan akwai ragowarsu , su daiji mai dame za'ayi yanzu kamin case ɗin yakai kotu.
 
 
 
★★★★★★
 
Ƙarfe 10am kuwa saiga su Yahanazu sunzo mana domin taya mu murna, daga bakinsu muke jin wai annemi Alh Bello da Alh Murtala tun jiya da rana anrasa.
 
Bance komai ba naja bakina na ɗinke sai dai abin yayi man tsaye a raina ina ayyana abubuwa da dama.
 
Sai bayan tafiyarsu nake gayawa Hajiya Inna, "Allah ya bayyana su" kawai ta ce taja bakinta ta tsinke, kamar yadda ta yi nima haka na yi.
 
Bayan an gama binciken su , sun tabbar dasu kaɗaine kuma kosu ƙaddara ce ta gitta masu a yi masu lamuni ba zasu sake ba.
 
Tafiyar su Baba ake gaya masu dole za'a tura case ɗin a kotu.
 
Sosai Baba yaso a bar abin basai anje kotu ba, amman jami'an tsaro suka ƙi.
 
Da wanna damar da Ya Haidar ya samu ya yanke shawarar shima shigar da tashi ƙarar ta kisan gillar dasu Alh Bello suka yiwa mahaifinsa.
 
Kai tsaye kuwa yaje kotu ya shigar da komai ya karɓo sammaci ya nufi gida.
 
Sumun abinda ke faruwa a cikin gidanne ya sanya jikinsa  yin sanyi , yaso a yi komai yanzu a wuce gurin kamin ya fara batun aurensa.
 
Dole ya adana takardar har izuwa lokacin da zasu bayyana , yaje ya ci gaba da gudanar da ayukkansa da kuma harhaɗa hujjojin da yake dasu.
 
 
                ★★★
 
*24Dec*
 
Yau ta kama 24Dec a yau za'a fara zaman kotu.
 
Bayan ya gama shirin fita yake sanar damu sosai muka dinga yi masu addu'ar samun nasara.
 
Yana fita daga cikin gidan station ya nufa, har yau baiga waƴanda aka kama ba, wato masu garguwarnsn.
 
Sosai ya cika da ɗunbin mamaki lokacin daya shiga cikin station ɗin, ganin Alh Bello da Alh Murtala tsaye a cikin wani hali a gaban motar jami'an tsaro.
 
 
Gunsu ya nufa yana tambayarsu "meya faru ya gansu a station" , duk da yadda zuciyarsa keyi masa tafasa idan ya gansu amman a haka ya cije ya yi masu maganar.
 
Ɗaya daga cikin jami'an tsaro ne yake sanar dashi ai sune waƴanda suka yi garkuwa da ƙannensa.
 
Sosai ya fiddo idanuwa waje gabansa na faɗuwa ya ce "waƴanmi ƙannen nawa?."
 
"Umar da Ahmad mana waƴanda a kayi garkuwa dasu a shekaran jiya", cewar jami'in tsaron kenan.
 
Kallonsu ya keyi cike da kiɗima, yayinda idanuwansa suke faman rufewa , lokaci ɗaya ya zube gurin ba alamun rai a tare dashi.
 
Cike da kiɗima jami'an tsaro suka kawo masa ɗauki gaggawa kai tsaye asibin dake cikin station ɗin aka nufa dashi.
 
Muna zaune labari yazo mana iya tashin hankali mun shigesa a haka muka taso muka zo station ɗin domin duba lafiyarsa.
 
Har muka zo bai farfaɗo ba, likita ya sanar damu firgici ne akwai abinda yaji ya kiɗimar dashi.
 
Jan hannun A'isha na yi naje gurin jamin'an tsaro ina tambayar su meya same sa?.
 
Gayamin abinda ya faru suka yi, ni kaina sai da naji hajijiya na neman kaini ƙasa, ba abinda bakina ke faɗa sai "innalillahi wa innah ilaihirraji un, allahumma ajirni fi musibatin".
 
Da jan ƙafa muka isa gurin dasu Hajiya Inna suke, komawa na yi gefe na yi zaune iname tananin anya mutanen ga suna tsoron Allah kuwa?.
 
Girgiza kaina na yi sannan na ce "waƴannan da gani ba ɗigon imani a cikin zuciyarsu".
 
"Ni dama nasan yadda nake ji idan naga Baba Murtala ya shiga sashen Hajiya Inna ba banza ba, dama shi Baba Bello baya shiga sashen nata.
 
Inanan ina tunanin lamarin ashe Hajiya Inna na saman kaina tana yimin magana ban jiba, sai ji nayi tana rafka salati a lokacin ne na dawo daga ƙauye dana lula, kallona nakai kansu jin yadda Hajiya Inna keta sabbatu na sheda A'isha ce ta gaya mata.
 
Banso tasan su bane domin ganin yadda tsufa ya zo mata kada wani abu ya dameta sai gashi sam na manta ban jawa A'isha kunne ba.
 
Banyi aune ba saiji na yi Hajiya Inna ta fashe da kuka tana roƙon Ubangiji Allah ya shiga tsakaninta dasu Baba Bello a kan sharrin da suke bibiyar zuriyarta da'ita.
 
Ni da Mama ne ke bata baki , ya yinda sai ci gaba da kuka takeyi tana faman ja masu Allah ya isa, abinka da tsufa.
 
Sai da muka yi dakyar sannan muka samu ta yi shiru amman duk da haka bakinta be mutu ba.
 
Munanan har 6pm har lokacin Ya Haidar be farfaɗo ba, sosai muka shiga cikin ruɗani , su Mama dai suka juya zuwa gida aka barni ni da Hajiya Inna duk da sun sanar damu basa buƙatar ƴan jinya amman ƙiri ƙiri Hajiya Inna taƙi yadda muje gida ta ce "ita kam ba inda zata Shalelenta yana kwance a gadon asibiti".
 
Anan waje muke har 11pm be farfaɗo ba, gashi ba wurin kwanciya, ai Hajiya Inna data ga ba sarki sai Allah dole ta ce dani na tashi muje gida.
 
Bakin titi muka fito muka tari napep , har bakin get ya kaimu na karbi ₦200 a gurin Baba mai gadi na bashi kasan cewar bamu fito dako fici ka ba.
 
Ciki muka nufa, a wannan daren duk yadda naso na runtsa Hajiya Inna hanani ta yi da jinininta , sosai kaina ke ciwo kasan cewar gajiyar dake tare dani ga bacci, yau ki manin kwanana uku ban runtsa ba kenan hwa.
 
Sai dana sulale na bar mata ɗakinta na dawo Parlour anan kan carpet na kwanta nice ban farko ba saida naji kiran salla a cikin kunnena.
 
Miƙewa na yi jikina gaba ɗaya sai ciwo ya ke yimin  a haka na watsa ruwa na yi sallah kana na fito na shiga kitchin.
 
Ƙarfe 7am na fito da shirina na zuwa asibiti, basket ɗin dana ajiye na ɗauko da sunan na fice bana son Hajiya Inna tasan gunda zanje , sai dai me?.
 
Muryarta naji daga baya na tana faɗan "idan kin shirya muje, nasan yanzu kam Shalelena ya farfaɗo kam".
 
Bance da'ita komai ba na yi gaba tana baya har yau maganar ɗaya ce saita sa Shalelenta ya kulle su Baba Bello.
 
Bance da'ita komai ba na isa gurin Baban Gida direba na gaya masa inda zamu.
 
Ko a mota haka Hajiya Inna ta yi ta jininin abin, ban daice da ita komai ba har muka isa.
 
Mun samu ya farfaɗo sai dai an hana mu shiga, a cewarsu yana buƙatar hutu.
 
Gefe muka yi zaune kowa da Abinda yake saƙawa a cikin ransa......
 
 
 
 
 
 
 
ƳAR MUTAN BUBARE CE