Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Ɗaya

Babban Buri:Fita Ta Ashirin Da Ɗaya
BABBAN BURI
 
 
 
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
 
 
 
 
 
بسم الله الرحمن الرحيم
 
 
FITOWA TA ASHIRIN DA ƊAYA
 
 
 
~~~A nan kan hanya kuwa suka hango mu, mu biyu duƙe a ƙasa muna faman kuka, da sauri suka ƙara so suna tambayar mu abinda ke faruwa.
 
A'isha ce ta yi ƙarfin halin sanar da su nikam lokacin na tabbata ko na ce na yi magana ba zan iya ba.
Iya tashin hankali kuwa sun shige sa najin abinda ya faru, sosai abin ya ɗaure masu kai, gaba ɗaya suka rasa wacce hanya ma za su bi.
 
Saurin fito da wayarsa daga aljihu ya yi , ya yi azamar dannawa jami'an tsaro kira bada jimawa ba kuwa nan danan zancen ɓatan ƴaƴan gidan margayi AS Wurno ya bazu a ko inah.
 
Haka muka ga wannan daren kamar yadda muka ga rana a zaune, tun ina kuka har hawayen suka daina fitowa.
 
Sai lokacin na samu zarafin bawa Ya Haidar lambar dana yi copying, haka aka bawa jami'an tsaro lambar domin sauka ƙawa.
 
Wasa wasa hwa mune har sahwa zaune muna rarraba idanuwa, amman ba labarin su Umar ko kaɗan sai faman kiraye kiraye da amsar waya da Baba da Ya Haidar ke yi.
 
Mama kam ba bakin magana , sai dai daka kalleta zaka tabbatar da bata tare da nutsuwarta.
 
Hajiya Inna kuwa har kuka sai da ta yi , kai duk wani me imani yaga yadda muke a wannan lokacin dole ne ya tausaya mana.
 
Ƙarfe 6am sai gashi ankira Ya Haidar domin neman kuɗin fansa recording ya sanya wayar mu kuwa muna kewaye dashi.
 
Sallama ya yi masu daga can ɓangaren muryar wani mutum ta ratso mu ta cikin wayar yana kwankwaɗar dariya.
 
Sai da ya yi me isarsa sannan ya dakata ya ce "ku daina wahalar da kanku gurin neman mu, munyi maku nisaa, abu ɗaya ne muke buƙata sune kuɗi kuɗi kuɗi, kamar yadda a halin yanzu bakwa da *BABBAN BURI* daya wuce kuga a yarin ƴaƴanku haka muma bamu da burin daya wuce muji lumus".
 
"Karku tayar da hankalin ku domin kuwa ba wasu kuɗine da yawa ba, ba yawa hwa miliyan takwas ne muke buƙata a gareku,  idan kun shirya ƙarɓar yaranku ku neme mu, idan har kuka haɗa wannan case da jami'an tsaro ba makawa kuɗin ku zasu lunku ne, duk abinda kuke yi a saman idanuwana kuke yinsa, nasan waƴannan kuɗin bakomai bane a gurinku domin kuwa kamin AS Wurno ya rasu ya ajiye maku fiye da rabinsu".
 
Ƙittt aka yanke wayar , danna kiran ya yi da sunan ya ce su bamu yaran muji muryar su  amman inaáh wayar a kashe take.
 
Wani kuka ne ya suɓuce mana a lokaci ɗaya dani da A'isha haɗi da Hajiya Inna, Baba kuwa ba abinda yake faɗa sai "ƙalu innalillahi wa innah ilaihirraji un!!!", Ya Haidar kam miƙewa ya yi tsaye yana safa da marwa, Mama kam tana zaune kanta a ƙasa ba zaka taɓa cewa tana gurin ba idan har baka kula da'ita ba.
 
Haka ma a wannan ranar a kayi ta nema amman shuru.
 
Tun safe rabona dana sa Ya Haidar da Baba a idanuwana ashe suna can gurin harhaɗa kuɗin da aka nema.
 
Sai 8pm suka shigo duk wanda ka kalla daga cikinsu ba zaka yi marmarin sake haɗa idanuwa dashi ba daga cikin su.
 
Lokaci ɗaya sunca ja, idanuwansu sunyi wani zurmawa suturar jikin su ma sai kunga yadda ta yi, kwallace me zafi ta silalomin a saman kunci ne.
 
Haƙiƙa ko su waye waƴannan mutanen ba zamu taɓa yafe masu ba, sun jefamu cikin tashin hankali marar misaltuwa.
 
Tare da kuɗin suka shigo suna jikin jikka ɗaya , waƴanda da kame kame da komai a kasamu kuɗin suka kai hakanan sai dai ko alama ba'a sayar da komai ba , cikin rufin asirin Allah aka haɗa su.
 
Da duk aka kira wayarsu bata shiga , haka muka yi zaman jiran wayar tasu , sai gashi kuwa 12am sun kira wannan karon ma dariya ce ta amsa sallamar da Ya Haidar ya yi, "ina fatan kin haɗa mana kuɗin mu zuwa yanzu?, gyaɗa kai Ya Haidar ya yi kamar suna ganinsa kana ya haɗiye waƴansu yawu da suka tarar masa cikin baki da ƙyar ya ce "insha Allahu, sai dai muna bukatar muji muryar yaranmu domin tabbatar da kune ko baku bane".
 
Nan danan kuwa saiga kukan Umar da Ahmad a cikin wayar kana daga bisani muryarsu ta ratso mu "Baba Baba Baba! Ya Haidar ku kawo mana ɗauki , zasu kashemu zasu......", Ƙit muryarsu ta ɗauke kana mukaji muryar wannan azzalumin mutum inji A'isha hwa, ya ce "ina fatan kunji kuma kun gasgata, mun baku yau zuwa gobe idan babu kuɗin to tabbas zamu aika su barzahu".
 
Baba ne ya samu zarafin yin magana "ina zamu kai kuɗin idan sun kammala?, nan ya gaya masu wurin da zasu haɗu kana be jira komai ba ya kashe wayar.
 
Kasan cewar basu samu gamsashiyar amsa ba ya sanya mu ƙara gyara zama muna masu zubar da hawaye.
 
Ƙarfe 6am kuwa saiga wani kiran daga gare su "ƙarfe 8pm yau ɗin nan ku tabbatar da kunje kun ajiye kuɗin a gurin da aka gaya maku, idan kuwa 9pm ta yi muka jiku shuru to tabbas 9:30pm zaku ga kawunan ƴaƴanku a cikin gidan ku".
 
Yana gama faɗa ya kashe wayarsa.
 
Mudai mun zuba takumi muna kallon ikon Allah.
 
Anan Ya Haidar ya fita  suka tsara yadda za'a tafiyar da komai ba tare da ansha waya wahala ba za'a kame su, dashi da wani abokinsa DPO.
 
Ko wannan yinin a haka mukayi sa, zan iya cewa tun lokacin da muke cikin wannan yanayin gaba ɗaya ba ɗaya daga cikin wacce ta leƙo mu daga  sashen matan su Alh Murtala, hakan kuwa ba ƙaramin mamaki ya bani ba.
 
Ko a cikin mazan ba kowa ya shigo ba, sai dai Alh Murtala shi a kullum sahwe ta Allah yakan shigo ya safe haka da maraice.
Sai dai na rasa meyasa bawan Allahn ga ɗaya ni bai kwanta min ba, duk da yake Yaya a gurin mahaifina , amman gaba ɗaya zuciyata sai ɗar ɗar take yi dashi.
 
Ƙawata Fateema da ƴan gidansu sunzo suka jajanta mana, suka tafi anan suka barta tayi mana yini, hakan kuwa ya yi matukar faran tamin ko bakomai zan samu wacce zata dinga lallashina domin kuwa a sashen mu ba wanda ke yin ta wani kowa ka gani sai addu'a.
 
Koda a kayi sallar magarib su Ya Haidar sun gama shirya komai, suna fitowa daga magrib suka ɗauki hanya domin zuwa kai masu kuɗi, dashi da Baba a cewarsu basa buƙatar sugan su sunzo da wani idan son samu ne ma karsu zo da kowa , idan aka samu matsala kuwa ba makawa zasu lunka masu kuɗi.
 
Tafe suke suna ƙara tattauna yadda abin zai kasance har suka isa surƙurmin dajin da suka ajiye anan zasu bada kuɗin a basu Ƴaƴan.
 
Ƙarfe 7:40pm suka isa dajin, dulum yake ba haske ko kaɗan a cikin sa a haka suka yi amfani da fitilun wayoyinsu wurin shiga cikin dajin.
 
A dai dai gurin da suka yi dasu za a kawo masu su Umar a dai_dai nan suka tsaya,  suna masu roƙon Allah nasara.
 
8:00pm sai ga wata baƙar mota ƙirin ko ina nata baƙi ne , ba zaka taɓa ganin wanda ke cikinta ba, ta parker ta gaban su, kuɗin Ya Haidar ya ɗauko dake cikin jakka ya nufi motar ya yinda Baba ya tsaya daga baya yana sarrafa wayarsa cikin taku da nuna kamar ba ita yake taɓawa ba, gilashin motar aka sauke sannan hannaye suka  ɓullo ta cikinsa, ɗaya bindiga ce ɗaya kuwa hannun ne kawai.
Ɗan daka tawa ya yi sannan cikin da kewa ya ce "ina yaran?",  Ƙofar motar a ka wangale saiga su Umar a tsaye gurin tare da wani wanda shima fuskansa take rufe gaba ɗaya kamar yadda ta ɗan uwansa take, tsaye tare dasu bindiga biyu riƙe da hannun sa.
 
Miƙawa wanda ya miƙo hannu jikkar Ya Haidar ya ta fiyi, shi kuwa wanda ke riƙe dasu Umar ya tunkuɗo su waje ya mayar da murfin motar ya rufe ya zaci kuɗin sun shigo.
 
Kamin suyi wani motsi jami'an tsaro sun kewaye motar basu lura ba, jikkar Ya Haidar ya sakar masa a saman hannu yana me sakar masa murmushin gefen baki.
 
Kamin kace kwabo anyi nasarar cafke su su biyu aka jefa su a cikin motar jami'an tsaro suka nufi cikin gari.
 
Hamdala Baba da Ya Haidar suka yi ta yi zuwa ga Allah kana suka taimakawa su Umar suka sanya su a mota aka zo dasu gida.....
 
 
 
Za mu cigaba gobe..........
 
 
 
 
ƳAR MUTAN BUBARE CE