Babban Buri:Fita Ta Ashirin

Babban Buri:Fita Ta Ashirin
BABBAN BURI
 
 
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
FITOWA TA ISHIRIN
 
~~~Bai jima ba ya fito hannunsa ɗauke da leda baƙa, shiga ya yi ya tada motar muka nufi gida.
 
A tsakar gidan ya yi parking sannan ya ce da A'isha taje ta kira su Umar su kwashi kayan.
 
Cikin gida ta nufa , wayar dake hannuna ya ƙarba ba tare daya ce dani komai ba, buɗe ta ya yi ya fito da sim card nawa ya mayar ya rufe.
Ledar daya shigo da'ita ya janyo ya ɗauko kwalin waya ya ɓallesa , saiga waya sabuwa dall da ita ƴar zamani wato tauching ya sanya min sim nawa a ciki sannan ya tura whatsApp ya buɗe min da kansa kana ya miƙomin wayar sabuwa da tsohur.
 
Tsare sa na yi da idanuwana sannan na ce "me hakan ke nufi?", "ban isa bane?", ya faɗa yana mai tsareni da idanuwansa.
 
Girgiza kai na yi sannan na ce "ban ce ba", "to karɓa".
 
Hannu biyu nasa na ƙarɓa sannan na hau yi masa godiya, farcensa ya ɗaura a saman  bakinsa sannan ya ce "bana buƙatar godiyar ki, domin kuwa ba wani abu bane dan Yaya ya yi wa ƙanwar sa wani abu ba".
 
"Haka zalika ba wani abu bane dan ƙanwa tace da Yayanta ta gode ba".
 
Ɗan murmushi ya saki sannan ya ce "kin ganki kuwa."
 
Sunne kaina ƙasa na yi sannan na ce "buɗe min mota na fita kar aga na jima ban shigo ba".
 
"Ai sunsan kina gun mijinki".
Saurin zaro idanuwa waje na yi na ce "ni dai rufamin asiri dan Allah ka buɗe min."
 
"Zan buɗe maki amman sai kince min I LOVE YOU".
 
"Wai meyasa ka cika yawan sa mutune magana ne?".
 
"Oho" , ya faɗa yana me kwantar da kansa saman kujera.
 
Ganin mun ɗauki lokaci a haka bashi da niyar buɗewa ya sanya ni cewa "I LOVE YOU" na yi maza na rufe idanuwana.
 
"Woww kiji yadda kalmomin suka fito daga bakin ki kuwa?, dan Allah maimaita naji."
 
"Dan Allah ka buɗe min kofa".
 
Buɗe wa ya yi bece komai ba na yi azamar ficewa daga ciki.
Ina fita naga Safiya tsaye a bakin sashensu tana aikomin da harara ba tare dana kula ta ba nayi shigewata sashen Hajiya Inna.
 
Saman kujera na zube ina faɗan "wash Allah na gaji".
 
"Aikin me kika yi kika gaji?", cewar Hajiya Inna.
 
"Kedai Hajjaju bari Allah yau munyi yawo sosai hwa", na faɗa iname daura mata wayar a saman cinyarta.
 
Washe haƙora ta yi sannan ta ce "ta waye?".
Cikin kunne na raɗa mata "Ya Haidar ya sayamin, ki ajiye ta a gunki idan Baba ya dawo ki nuna masa sannan ki nunawa Mama."
 
"Oh ke meyasa ba zaki nuna masu bane?".
 
"Kunya na keji Hajiya Inna".
 
"Oh kenan nice ba kyajin kunya ko?".
 
"A'a Hajiya ba haka bane kawai dai kawai dai", na faɗa ina mesa dariya.
 
"Ja'irar yarinya zakiyi bayani ai, ni bara shi Baban naku ya shigo ma na gaya masa ni dai na gaji da shirmen ku , ayi lamarinnan da wuri na huta, ko ɗazu hwa ina ganin ku ta ƙasan ido kuna yiwa mutane rashin kunya gurin cin abinci".
 
"La la lah Hajiya Inna yaushe kika fara sa'ido?."
 
"Yau ɗinnan" ta faɗa tana faman daƙilar waya.
 
★★★★★★
 
Bayan mun kammala sallar isha'i, naje na shirya kayan da muka siyo , a cikin ɗakin dake sashen Mama naje na shirya kayana kaf na kwashi na A'ishah naje ɗakin Hajiya Inna na shirya mata.
Domin kuwa nikam Allah ya gani bazan iya zama da Ya Haidar a guri guda ba, gwanda mu dinga nesa nesa da juna.
 
Wuraren ƙarfe 9pm Baba ya dawo daga fitar da ya yi shida Baban Gida direba a sashen Mama yaci abinci sannan ya shiga sashen Hajiya Inna lokacin ina cikin ɗakinta inajinta tana faɗa masa ya san akwai alaƙa a tsakaninmu kuwa?, amsar daya bata ce ta sanya ni naji kunya sosai "na daiga alamu daga jiya zuwa yau" ya faɗa yana kallonta.
 
Ji na yi kamar na nutse daga gurin da nake , "ai kuwa ya zamo dole na gujewa haɗuwa da Ya Haidar" na faɗa a cikin raina.
 
Basu tashi daga gurin ba sai da suka tattauna sosai a kan maganar mu da Ya Haidar.
 
Sosai naji daɗin abin ko bakomai nima zan cika BURIN dako wacce ɗiya mace take dashi a rayuwarta.
 
Duk da bansan yadda ake aiki da irin wayoyinnan ba , hakan be hanani ɗan dan gwalawa ba sai gashi ina fahimtar komai da komai daki daki.
 
Haka wuraren 10pm ya kirani a waya kan cewa na hau whatsApp.
Kasancewar nasan ana buɗe data idan za'ayi chat ya sanya ni nemanta da yake ina iya rubutawa da kuma karantawa duk da banyi  wani karatu me zurfi ba kuwa.
 
Tunanin karatun A'isha na fara wanda har yau ina nan da Burin son naga ta yi karatu sosai , a rayuwata bani da *BABBAN BURI* daya wuce a ce yau naga A'isha ta samu ilimi me zurfi, a ko wacce safiya ina rokon Allah ya cika min wannan Burin nawa.
 
Sai gashi ni dake bacci ƙarfe 9pm yau na kai har ƙarfe 12am idanuwana biyu, hakan kuwa ba ƙaramin mamaki ya bani ba, a zuciyata na ce "wani abu sai SOYAYYA."
 
 
A sashen Hajiya Inna bacci ya ɗauke ni wanda bansan lokacin daya samu nasarar ɗauke ni ba.
 
#Asuba ta gari KhadynHaidar<img class="an1" style="width: 1.2em; height: 1.2em; vertical-align: middle;" aria-label="