Babban Buri.......

Tun 7am muke faman dafe dafen abinci mune har 12pm ba mu kammala ba. A dai dai lokacin da muke ƙoƙarin kwashe tukunyar ƙarshe ne mu ka ji hayaniyar ƴan gidan cikin babban Parlour.

Babban Buri.......

BABBAN BURI.


MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.


Dukkanin Godiya ta tabbata ga Allahu subhanahu wata'ala, tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Manzon tsira MUHAMMADUR RASULULLAHI S.A.W.

Wannan littafin ƙirƙirarren labarina ban yi dan wata ko wani ba, idan har kika ga ya yi dai dai da irin rayuwarki so arashine kawai amma ba don an yi saboda ke ko kai ba.

Kar ki kuskura ki juyemin labari idan kuwa har hakan ta kasance za mu rabu da wanda ya yi haka dutse hannun riga.

Ina roƙon Ubangiji Allah ya sa abin da zan rubuta ya amfanar da al'umma, Allah Ya kare min hannuna da kuma alƙalamina da rubutu taɓara, Allah Ya sa wannan littafin al'ummar annabi su ƙaru da darussan dake cikinsa.


SADAUKARWA ZUWA GA : AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU} MARUBUCIYAR {MATAR ABDALLAH}.


FITOWA TA ƊAYA.


بسم الله الرحمن الرحيم

~~~Duk da tsantsar iskan dake faman kaɗawa wannan bai sanya ni a jiye sharar da nake yi ba, yi nake yi sai faman dawowa baya take yi a haka na kammala sharar  nakan dawo baya domin kuwa bani da burin daya wuce naga na kammala.

Ina ƙare sharar na yi a zamar janyo ruwa a cikin rijiyar dake malale a tsakar gidan mu , a hakan da sanyi su da komai na je na yi wanka da su.

Da sauri na kammala abin da nake yi na fito daga ɗakinmu , haɗi da janyowa 'yan ƙannena ƙafa, da 'yar touch ɗita ina haskawa na nufi ɗakin mama , haɗi da yin sallama a bakin ƙofar ɗakin, izinin shiga ta bani sauri-sauri na shiga ɗakin haɗi da ƙara yin wata sallamar , zaune take a saman darduma hannunta riƙe da carbi tana jaa, ɗaro da kanta tayi ta zuba min idanuwa , wayarta ta janyo ta duba gaban wayar sannan tayi a zamar kallona tace " ƙarfe shida da rabi zaki fita yau?", Gyaɗa mata kai nayi cike da ƙosawa domin kuwa na matsu ta bani hanyar da zan wuce domin kujewa cin zarafi a gurin aiki na.

"Mama yau ƴaƴan gidan waƴanda ke karatu a ƙasashen ƙetare ne zasu dawo, tun jiya suka ce karnayi lattin shigowa yau dan ayukkane dasu."
Gyaɗa kanta tayi alamar gamsuwa sannan ta ce "Allah ya tsare hanya ya baki abinda kike nema , ina roƙon Ubangiji Allah ya kawo maki mijin aure kije ɗakinki kema kiyi bautar aure ki huta da wannan wahalar da kike yi."

Cike da jin daɗin addu'ar Mama haɗi da kunya na amsa da "Amin ya Allah Mama".

Sallama nayi mata yayinda ita kuwa ta biyoni da kallon tausayawa haɗi da sanya hannunta ta sharce ƙwallar data samu damar silalowa daga kan kuncinta.

Ficewa nayi daga gidan namu a cikin dungu dungun safiyarnan na doshi gidan da nake aiki.
Har na gama ratsa unguwannin dake tsakanin gidanmu da gidan aikina ban haɗu da kowa a kan hanya ba, Kasan cewar ana faman surfa sanyi a lokacin gashi kuma safiya ce tsantsa bugu da ƙari gashi yau ranar ƙarshen mako ce wacce Bature ya ke cewa weekend, wato yau muna assabar.

Ƙwankwasa ƙaramin ƙauren ƙofar shiga gidan nayi sannan na ƙame a guri ɗaya ina rarraba idanuwana a cikin unguwar duk da yake ba wannan ne karo na farko dana fara shigowa unguwar ba amman sai da na tsaya ƙarewa maka makan gidajen dake a jiye a muhallan su kallo.
Tsit unguwar take baka jin motsin komai sai kukan karnuka dake faman tashi a cikinta , yayinda ko wanne gida yake ƙargame da alamu kam masu gida jen basu buɗe ƙofofinsu ba.
Jin motsin janye sakata ne yasan yani mayar da hankalina kan ƙauren gidan da nake tsaye.

Baba me gadi ne ya leƙo kansa daga cikin gidan yana faɗan "waye anan?", Saurin amsa masa nayi da "nice Baba", haɗi da ƙara matsar da fuskata dai dai gunda zai ganni.
Washe haƙoransa ya yi yana faɗan" a'a ƴar albarka ce yau da sanyin safiyar nan?."

Kutsa kaina nayi a cikin gidan haɗi da basa amsar tambayarsa ba "eh Baba nice".
Hanya ya bani yana mai tambayata ya muka tashi a gidan namu da kuma sanyinnan¿.

Cike da kulawa nake amsa masa , haɗi da dosar ainihin ƙofar shiga gidan.

Gida ne mai girman gaske wanda yake ɗauke da part part da yawan gaske ni kaina bazance ga adadin part ɗin dake cikinsa ba.
Daga shigar ka ainihin ƙofar farko ta gidan zaka ci karo da tsala tsalan motoci dake ajiye a muhallin da aka tanadar masu, sai kuma part part dake birjik a ko wanne lungu da saƙo na gidan, daga tsakiya kuwa ƙofar shiga ainihin babban Parlourn gidan ce wanda girman Parlourn zai isa a gina ɗan madai daicin gida mai ɗauke da ɗakuna a ƙalla uku da banɗaki haɗi da kitchine, maka makan kujeru ne zube a cikin ɗakin a ƙalla zasu kai set uku , Sai lallau san carpet ɗin da ke malale a tsakiyar ɗakin, daga damansa kuwa make ken kitchine ne wanda yake ɗauke da na urori kama da na ƙasashen waje har izuwa na ainihin ƙasarmu ta gado wato Nigeria.

Kitchine wanda ya tsaru iya tsaruwa ko wanne ɓangare da abinda ake ajiyewa a gurin m, sai kuma ɓan gare ɗaya da aka ware domin sarrafa a bincin da al'ummar gidan zasu antayawa cikinsu.
Sai kuma part ɗin masu aiki dake a gefen daman kitchine ɗin.

Jin gidan tsit ya tabbatar min da cewa lallai masu gidan basu tashi daga bacci ba.
Kai tsaye kitchine na nufa domin ganin me dame aka fara aiwatarwa.

Kiciɓis mukayi nida Hanne dake ɗauke da bokitin morping da alamu babban Parlourn gidan ta dosa.

Gaisawa muka yi sannan na tambayeta saura ƴan uwana waƴanda muke aikin kitchine a tare dasu.

Bayana ta nunamin ai kuwa ina juyawa naci kiciɓis da Yahanazu.
sallama na yi mata kana na nufi kitchine ɗin, kallona Yahanazu ta yi sannan ta ce "Yarinya kin makara ki ɗai juya."

Ƴar hararar wasa na sakar mata sannan na ce "wacce makara kuma?, Nidai bani hanya na wuce na gaji da tsayinnan."
Ɗan kaucewa daga kan hanyar ta yi tana tambayata ya kwanan su Mama.

Amsa mata nayi da lafiya kalau ina me miƙa mata ƴar jikkata dana sanya zane na da fitilata a ciki.

Sashen da muke abinci na nufa, ai kuwa na isko Rafi'a tana ta kai da kawowa a gurin.
Gaisawa mukayi da'ita sannan na kama aikina nima.
Cikin ƙanƙanin lokaci muka kammala abincin ƴan gidan sannan muka koma kan na baƙin mu.

Tun 7am muke faman dafe dafen abinci mune har 12pm bamu kammala ba.
A dai dai lokacin da muke ƙoƙarin kwashe tukunyar ƙarshe ne mu kaji hayaniyar ƴan gidan cikin babban Parlour.

Da hanzarin mu muka kammala kwashe abincin muka fice daga kitchine ɗin ko waccenmu hannunta riƙe da ƙaruwar colar muka doshi hanyar Parlourn.
A dai dai tsakiyar ɗakin muka ci karo da ledar cin abinci malale a gurin da hanzarin mu muka ajiye kulolin a wurin haɗi da kwaso plate plate nacin abinci da cokalayya muka ajiye a gurin , sannan muka kama gabanmu.

Abinci muka zuba wa sauran ma'aikan gidan kama daga masu bawa flower ruwa har izuwa direbobin gidan duk sai da muka zubawa ko wanne nasa a cikin muhallinsa kana Yahanazu ta ɗauka ta kai masu, zuba namu mukayi mu uku muka raɓe a gefen kitchine ɗin muka fara ci.
Muna kammalawa nayi sashen Hajiya Inna wacce itace uwa a gurin mazan gidan kaka a gurin jikokin gidan da aƙalla zasu kai 80 idan basu haura ba.
Dattijowa me mutunci da sanin ya kamata , tun zuwana gidan muke da sawa da'ita ko miye za'ayi mata nice take kira nayi mata shi, hakan kuwa baya taɓa ɓatamin rai.

Part ɗinta na shiga, tana gishin giɗe hannunta riƙe da littafin addu'oi.
Dai dai gunda ƙafarta take naje nayi zaune haɗi da gaidata , amsawa tayi cike da farin ciki sannan tace "yanzunnan nake niyar aikawa a kiramin ke kuwa kizo kiɗan murzamin maganainnan a ƙafafuwana gasunan sai faman zugi suke yi."

Ƴar dariya nayi kana nace "Wai Hajiya Inna meke sanya ƙafafuwanki ciwo ne?", Kedai bari Allahu a'alamu , inajin ciwon tsufa ne kawai." Kinga yanzu haka nayi niyar nabi a yarin ƴan gidannan domin in tarbo shalelena a airport amman ƴaƴannan suka rufe idanuwa suka hana."
Kallonta nayi sannan nace "laaah yanzu Hajiya Inna da zasu barki za ki je kuwa?".
Gyaɗa kanta ta yi alamar tabbarwa kana ta ɗaura da ce wa" Sosai kuwa badan komai ba saidan na tarbo ɗan gaban goshina HAIDAR nayi kewarsa sosai da sosai kinsan yanzu shekarunsa takwas a can ƙasashen turawannan ni narasa me yakeyi a can duk wadannan shekarun."
Amsar maganin nata nayi na fara murza mata shi a ƙafa na ce "shin shi kaɗai ne a can hakan?." Ina fa su shida ne a can amman sauran dukansu ƙannansa ne."
"Ayyah , ashe yau gidannan namu muna da manya baƙi har turawa", na faɗa iname rike baki na da hannu.

Ƴar dariya ta yi sannan ta ce "kin ji ki da wani zance kuma."Allah kuwa Hajjaju.".....


ƳAR MUTAN BUBARE CE.