An Yi Kira Ga Gwamnatin Zamfara Ta Taimakawa Mutanen Shinkafi A Halin Rashin Tsaro Da Suke Fama Da Shi 

'Yan taadda suna cin karen su babu babbaka a wadannan manyan hanyoyi biyu kusan kowace rana, a kullun sai an tare matafiya kuma an yi garkuwa da su, Idan aka yi rashin sa'a ma, wadanda aka yi garkuwa da su suna mutuwa a hannun 'yan taaddar. Kullun al'amarin kara lalacewa yake yi, mutanen Shinkafi sun zama wata saniyar ware, an raba su da sauran al'ummar Jihar Zamfara, ba tare da damar amfani da waya ba tun 3rd September, 2021, abin ban haushi, ba wanda ya damu da halin da muke ciki. Ina kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da tayi duk abunda ya dace domin ta fitar damu daga cikin kuncin rayuwar da muke ciki. Babban makasudin kowace gwamnati, wadda tasan abun da take yi, shi ne samar da tsaro da walwala ga al'umma. A duba Sashe na 14(2)(b) na Kundin tsarin Mulki na Nijeriya na 1999.

An Yi Kira Ga Gwamnatin Zamfara Ta Taimakawa Mutanen Shinkafi A Halin Rashin Tsaro Da Suke Fama Da Shi 

 

Shekaru da dama, Karamar Hukumar Mulki ta Shinkafi tana fama da matsalar tsaro. 

Ta yi suna wurin noma da kasuwanci. Wannan ya zama tarihi a yanzu. Babu mai zuwa gona ba tare da izinin yan taadda ba, hanyar Kaura- Namoda zuwa Shinkafi mai tsawon kilometer 50 ta zama tarkon mutuwa, daga Shinkafi zuwa Isa zuwa Sokoto, mai tsawon kilometer 120 tafi hadari. 

'Yan taadda suna cin karen su babu babbaka a wadannan manyan hanyoyi biyu kusan kowace rana, a kullun sai an tare matafiya kuma an yi garkuwa da su, Idan aka yi rashin sa'a ma, wadanda aka yi garkuwa da su suna mutuwa a hannun 'yan taaddar. Kullun al'amarin kara lalacewa yake yi, mutanen Shinkafi sun zama wata saniyar ware, an raba su da sauran al'ummar Jihar Zamfara, ba tare da damar amfani da waya ba tun 3rd September, 2021, abin ban haushi, ba wanda ya damu da halin da muke ciki.
Ina kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da tayi duk abunda ya dace domin ta fitar damu daga cikin kuncin rayuwar da muke ciki.
Babban makasudin kowace gwamnati, wadda tasan abun da take yi, shi ne samar da tsaro da walwala ga al'umma. A duba Sashe na 14(2)(b) na Kundin tsarin Mulki na Nijeriya na 1999.

A matsayina  dan kasa, wanda ya damu da halin da ake ciki, ina bada shawara ga gwamnati, da ta duba yiyuwar tunanin wasu hanyoyi, a mataki na gajeren zango, da matsakaicin zango da dogon zango wurin tsara jaddawalin samar da tsaro a wannan jiha ta Zamfara. Matakin Soja kawai ba zai yi maganin matsalar ba, yana da kyau, gwamnati ta samar da abubuwan more rayuwa a karkara, kamar hanyoyi, ruwan sha, wutar lantarki, wadataccen abinci, ilimi, tallafi ga mata da matasa da tallafin karatu ga dalibai. Yana da kyau gwamnati ta farfado da masana'antun mu da wurin koyon sanaoin hannu domin samar da ayukka ga dimbin matasan mu da basu da ayukkan yi.
Ta wannan hanyar kawai za'a samar da tabbataccen zaman lafiya mai dorewa a Jihar Zamfara. < /div>
 
Bello Galadi 
6th December, 2021